Gwamnan Katsina ya goyi bayan El-Rufai, Ganduje da Zulum a kan wanda zai gaji Buhari
- Aminu Bello Masari ya na goyon bayan mulki ya bar yankin Arewa a 2023
- Gwamnan Jihar Katsina ya ce adalci shi ne ‘Yan Kudu su dana mulkin kasar
- Masari ya ce kokarin Gwamnatinsu zai ba jam’iyyar nasara a zabe mai zuwa
Mai girma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce kamata ya yi mulkin kasar nan ya koma zuwa ga yankin kudancin Najeriya a 2023.
An rahoto gwamnan a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, 2021, ya na wannan kira a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV.
Gwamnan ya ce: “Game da batun karba-karba, adalci dai shi ne adalci. Idan ka tambaye ni, a matsayina na karon kai-na, ina tunanin ya kamata mu kai kujerar shugaban kasa zuwa yankin kudancin kasar nan.”
KU KARANTA: PDP ta nemi a gyara kundin tsarin zabe kafin 2023
Ko da gwamnan ya yi magana ne a matsayinsa na Aminu Bello Masari, bai bayyana shirin da jam’iyyarsu ta APC ta ke yi a game da zaben na 2023 ba.
Jawabin gwamna Aminu Bello Masari ya zo ne jim kadan bayan kwamitin PDP ya bada shawarar a bude wa kowa kofa ya nemi takarar shugaban kasa.
Wasu su na ganin idan 2023 ta zo, lokaci ne da Ibo zai samu damar zama shugaban farar hula a karon farko, wasu kuma na ganin Yarbawa sun fi cancanta.
Da aka tambayi Aminu Bello Masari a game da yankin da ya fi dace wa da mulki tsakanin bangarorin Kudun, sai kurum ya ce: “Kudu dai kudu ce.”
KU KARANTA: Sanatocin da su ka kwallafa rai da zama Gwamnonin Jihohi a 2023
Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar ya na ganin cewa jam’iyyar APC za ta samu nasara a zabe mai zuwa saboda tsare-tsaren da gwamnatinsu ta kawo.
Masari ya ce babu jam’iyyar da ta yi wa talakan da ba kowa ba tasiri irin APC ta hanyar kawo shirin da su ka inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa hali.
“Babu gwamnati ko jam’iyyar siyasa tun da aka samu ‘yancin kai da ta kawo tsare-tsaren inganta rayuwar mutane irin APC. An batar da biliyoyi a kan talakawa.”
A makon nan labari ya zo maku cewa akwai yiwuwar jam'iyyar hamayya ta PDP za ta sake ba ‘Dan siyasar Arewa takarar Shugaban kasa a zabe da za ayi a 2023.
Wani kwamitin PDP ya ce idan da gaske su na neman karbe mulki, sai sun dirje ‘dan takarar da ya dace, ba tare da la'akari da wani bangare na kasar nan ya fito ba.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng