Siyasa: Jerin fitattun ‘Yan Majalisar Dattawa 10 da su ke harin kujerar Gwamna a zaben 2023

Siyasa: Jerin fitattun ‘Yan Majalisar Dattawa 10 da su ke harin kujerar Gwamna a zaben 2023

Duk da daraja da albashi mai tsoka da ake samu, ba bakon abu ba ne a ga Sanata a Najeriya ya hakura da kujerarsa, ya tafi neman takarar kujerar gwamna.

Yayin da wasu ke fara sharan-fagen zaben 2023 tun yanzu, ana kyautata zaton akwai wasu Sanatocin da su ke harin takarar gwamna a zabe mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu Sanatoci da ake ganin idon su ya na kan zaben gwamna:

1. Enyinnaya Abaribe

Sanata Enyinnaya Abaribe kwararren ‘dan siyasa ne wanda ya yi mataimakin gwamna a Abia. Ana ganin cewa Sanatan na PDP zai nemi ya gaje kujerar gwamna Okezie Ikpeazu a 2023.

2. Ike Ekweremadu

Ike Ekweremadu mai shekaru 58 a Duniya ya rike mukamai da dama a siyasa. Masu hasashen siyasa sun ce kwararren Lauyan zai so ya yi takarar gwamnan jihar Enugu a zabe mai zuwa.

3. Emmanuel Bwacha

KU KARANTA: Ministocin tarayya masu shirin takarar gwamna a 2023

Siyasa: Jerin fitattun ‘Yan Majalisar Dattawa 10 da su ke harin kujerar Gwamna a zaben 2023
Sanata Elisha Abbo zai nemi Gwamna Hoto: @AbboElisha
Asali: Twitter

Wani Sanata da ke jerin na mu shi ne, Emmanuel Bwacha mai wakiltar kudancin jihar Taraba a majalisar dattawa. Watakila Sanatan ya yi takarar neman gwamna a karkashin PDP a 2023.

4. Ovie Omo-Agege

Ovie Omo-Agege mai shekara 57 shi ne na hudu a jerin. Tauraruwar ‘dan siyasar ta na cigaba da kara haske tun da ya dawo APC, akwai yiwuwar ya na harin kujerar Ifeanyi Okowa a Delta.

5. Ishaku Elisha Abbo

Sanata Ishaku Abbo mai wakiltar Arewacin jihar Adamawa a majalisar dattawa bai boye sha’awarsa na takarar gwamna ba, a dalilin haka ne matashin ya bar jam’iyyar PDP.

6. Abba Moro

Tsohon Ministan harkokin cikin-gida, Abba zai iya neman takarar gwamnan jihar Benuwai kamar yadda abubuwa su ke nuna wa. Moro ya fito ne kabilar Idoma, masu rinjaye a jihar.

KU KARANTA: PDP: Atiku, Kwankwaso za su iya kai labari a zaben 2023

7. Kabiru Ibrahim Gaya

Fitaccen Sanatan Kano, Kabiru Gaya zai iya takarar gwamna a 2023. Gaya zai so ya koma kujerar da ya lasa zakinta a 1992, kafin gwamnatin soja ta sauke duka gwamnonin jihohin kasar.

8. Barau Jibrin

Wani Sanata da ke tunanin zai nemi kujerar gwamna a Kano shi ne Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa. Barau ya fito daya ne da gwamna Abdullahi Ganduje.

9. Ahmad Babba Kaita

Magoya-bayan Sanata Ahmad Babba Kaita su na so gwanin na su ya tafi gidan gwamnan jihar Katsina bayan ya rike kujerar ‘dan majalisar wakilai da dattawa a karkashin APC.

10. Uba Sani

Wanda mu ka rufe jerin da shi a nan ba kowa ba ne faceUba Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya. Alamu na nuna tsohon hadimin gwamnan Kaduna zai jarraba wata sa’ar a 2023.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng