Abin Da Yasa Ba Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Nigeria ba, Gwamna Wike

Abin Da Yasa Ba Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Nigeria ba, Gwamna Wike

- Nyesome Wike, gwamnan jihar Rivers ya ce matsalar yan bindiga ba zai kare a Nigeria ba

- Wike ya ce gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar APC ta siyasantar da batun tsaro hakan yasa ba a samun nasara

- Wike ya ce a shekarar 2015 ya tafi wurin gwamnatin tarayya neman taimako kan tsaro amma aka hana shi saboda siyasa

Gwamnan jihar Rivers, Chief Nyesome Wike ya yi bayanin cewa abinda yasa aka gaza kawo karshen yan bindiga shine saboda gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na cigaba da saka siyasa cikin batun tsaro.

Wike ya ce a yayin siyasantar da batun tsaro, gwamnatin APC ta saka matsalar tsaro a wasu jihohi ya munanana ta yadda ba za a kawo karshensa nan kusa ba, rahoton Vanguard.

KU KARANTA: Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021

Abin Da Yasa Ba Za a Iya Kawo Karshen Yan Bindiga a Nigeria ba, Wike
Abin Da Yasa Ba Za a Iya Kawo Karshen Yan Bindiga a Nigeria ba, Wike. Hoto: @Vanguardnewsngr
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da mai taimaka masa na musamman kan kafafen watsa labarai, Kelvin Ebiri ya fitar.

Wike ya yi bayanin cewa a shekarar 2015 lokacin da jiharsa ke fama da kallubalen tsaro, ya garzaya wurin gwamnatin tarayya amma a maimakon taimakonsa sai ta yi watsi da shi tana nufin ganin ya kasa mulkar jihar.

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Ya ce, "Ba su turo wa Rivers jami'an tsaro na musamman ba kamar yadda suka tura wa wasu jihohin. Sun ki taimako na saboda suna son in kasa mulkar jihar.

"Laifi bai san iyaka ba. Tana iya shafan ka gobe. Idan ta suna da niyyar yaki da laifi ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasa ba yanzu an samu sakamako mai kyau.

"Hare-haren yan bindiga ba zai taba kare wa ba tunda sun siyasantar da batun tsaro. Na fada musu kada su saka siyasa a batun tsaro.

"Yanzu suna girbar abinda suka shuka. Idan ka shuka zaman lafiya, za ka girbi zaman lafiya, idan ka shuka rikici, rikicin zai kasance tare da kai."

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel