Bayan shekaru 5 da sakinta, mata ta koma gidan tsohon mijinta ta lakaɗawa amaryarsa duka
- Matar aure ta yi karar tsohuwar matar mijinta a kotu da kawarta kan cewa sun bi ta gidan miji sun mata duka
- Wadanda aka yi kararsu, Ruka Tayo da kawarta, Jimoh Abiola, sun musanta aikata wannan laifin
- Alkalin kotun ta bada belin wadanda aka yi karar kan kudi 50,000 kowannensu ta dage cigaba da shari'a zuwa ranar 31 ga watan Maris
An gurfanar da wata mata mai shekaru 35, Ruka Tayo da kawarta, Jimoh Abiola, mai shekaru 35 a gaban kotun Majistare da ke Ikorodu a ranar Juma'a 12 ga watan Maris saboda yi wa amaryar tsohon mijinta duka.
An ce Tayo da kawarta sun yi wa wanda ta shigar da karar duka a gidan tsohon mijinta da ke Ikorodu, shekaru biyar bayan ya sake ta, The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS
Ana zargin matan biyu da laifuka biyu da suka hada da hadin baki da duka. Amma sun musanta aikata laifukan biyu.
Mai shigar da kara, ASP Gbemileke Agoi, ta shaidawa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 26 ga watan Fabrairu misalin karfe 4 na yamma a gidan mai lamba 7 Mowowole Estate, Oreta Igbogbo, Ikorodu.
Agoi ya yi zargin cewa wadanda aka yi kararsu sun hada baki sun yi wa wanda ta yi karar duka, wata Mrs Adeyemi Morenikeji, a gidan mijinta saboda tana auren tsohon mijin daya daga cikin wadanda aka yi kararsu.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 41, sun ceto mutum 60 a Borno
A cewarsa laifin ya saba wa sashi na 412 da 172 na dokar masu laifi na jihar Legas, 2015.
Alkalin kotun, Mrs R.A. Onilogbo ta bada belin wadanda ake zargi kan kudi N50,000 kowannensu da mutane da suka tsaya musu.
Ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Maris.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng