Okonjo-Iweala ta fadawa Buhari hanyar da zai bi, ya gujewa sake aukawa matsin tattalin arziki
- Shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta ba Gwamnatin Tarayya shawarwari
- Ngozi Okonjo-Iweala ta bukaci Gwamnati ta rage dogaro da arzikin man fetur
- Okonjo-Iweala ta ce nan gaba za a rage bukatar amfani da mai a fadin Duniya
The Nation ta ce a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta fadi hanyoyin da Najeriya za ta bi ta tsira daga shiga cikin matsalar tattali.
Darekta-Janar ta WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta ce ya zama dole gwamnatin tarayya ta fadada hanyar samun arzikin Najeriya, sannan a tsaya tsayin-daka.
Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa sai Najeriya ta rungumi cigaba ta bangaren fasahar zamani.
Shugabar kungiyar kasuwancin Duniyar ta yi gargadi cewa idan ba a dauki matakin rage dogaro da arzikin man fetur ba, Najeriya za ta gamu da matsin lamba.
KU KARANTA: Kudin da su ka fi kowane daraja a Afrika
Tsohuwar Ministar kudin kasar ta yi kira: “Mu na bukatar mu samu dabarar tattalin arziki da za mu guje wa dogaro da abu daya wajen samun kudin shiga.”
Jaridar ta rahoto cewa Okonjo-Iweala ta na yabon kamfanin Dangote da irin kokarin da yake yi musamman a kan matatar danyen man fetur da yake gina wa.
Sabuwar shugabar ta WTO ta ba Najeriya shawarar ta koma wa wasu hanyoyin samun karfin mai domin wasu kasashe su na kokarin daina amfani da man fetur.
“Dole mu canza akalar gwamnati yadda tattalin arzikinmu zai rika samar da ayyukan yi, ya kawo mana kudin kasar waje.” Ta ce wannan shi ne abin da ya dame ta.
KU KARANTA: ‘Yan kasuwa su na kuka, farashin kayan gwari ya yi raga-raga
Masaniyar tattalin arzikin ta bada shawarar a tsaida farashin canjin kudin kasar waje, sannan ta yi magana a kan yadda Najeriya za ta shawo kan annobar COVID-19.
Okonjo-Iweala ta yi magana ne da ‘yan jarida bayan ta gana Mai girma Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, inda ta yi masa godiya na alfarmar da ya yi mata.
A jiya kun ji cewa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta ziyarci shugaban kasa Muhammad Buhari a karon farko bayan ta dare kujerar WTO inda aka kai ruwa rana ana takara.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta taimakawa Okonjo-Iweala a takarar da ta yi a shekarar bara.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng