Sabon shugaban hafsun Sojojin Najeriya ya ce an kusa gama yakin Boko Haram

Sabon shugaban hafsun Sojojin Najeriya ya ce an kusa gama yakin Boko Haram

- Janar Ibrahim Attahiru ya ziyarci wasu Dakarun Sojoji da ke yakin Boko Haram

- Shugaban hafsun sojojin kasan ya ce an kusa ganin karshen fafatawar da ake yi

- COAS Ibrahim Attahiru ya yabi Sojojin, ya yi alkawari zai share masu hawayensu

Shugaban hafsun sojojin kasa, Laftanan-Janar Ibrahim Attahiru, ya yi magana a game da yakin da ake yi da ‘yan ta’addan Boko Haram a Najeriya da kewaye.

Jaridar Punch ce ta rahoto Laftanan-Janar Ibrahim Attahiru ya na tabbatar wa dakarun sojojin kasa cewa yakin na Boko Haram ya kusa zuwa karshe.

Da yake jawabi a karshen makon da ya gabata, Janar Ibrahim Attahiru ya ce an kusa gama yakin.

Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana haka ne yayin da ya kai wa wata runduna ta Operation Lafiya Dole ziyara a garin Damuturu, jihar Yobe a ranar Lahadi.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa

Ya ce: “Mun zo jihar Yobe ne domin mu gana da ku, mu sanku, kuma ku sanmu. Mun yi maku alkawarin kawo karshen wannan lamari na Boko Haram.”

“Ina kawo maku gaisuwa ta musamman daga shugaban kasa kuma shugaban dakarun sojojin Najeriya, ya samu labari, kuma ya san da aikin da ku ke yi.”

Janar Ibrahim Attahiru ya ke cewa: “Ina so in fada maku, a matsayina na shugaban hafsun sojojin kasa, na zo ne domin in ji irin kalubalen da ku ke fuskanta.”

Ibrahim Attahiru ya ce zai tabbattar da cewa an yi maganin koken sojojin kasan na shi domin ya karfafa masu gwiwa su yi aikinsu na tsare al’ummar kasa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barna, sun hallaka Jami'in tsaro a Najeriya

Sabon shugaban hafsun Sojojin Najeriya ya ce an kusa gama yakin Boko Haram
Janar Ibrahim Attahiru
Asali: Twitter

Attahiru ya nuna ya ji dadin aikin da sojojin su ke yi, ya ce ya na alfahari da dakarun ‘Operation Tura Ta kai Bango' da su ka fatattaki ‘Yan ta'addan Boko Haram.

“Mu na alfahari da ku, kuma na yi imani cewa a zagaye na biyu na wannan aiki, za ku kara kokari.”

Kwanaki kun ji labarin wani sabon bidiyo da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta fito, inda aka ga wasu kananan yara da ake koyar da su addini da dabarun yaki.

A faifen bidiyon mai tsayin mintuna kusan 17, an ga kananan yara na koyon harbe-harbe da fada.

An ga wasu daga cikin wadannan kananan yaran rike da wani irin katako da aka yi masa irin kirar wata bindiga mai suna Kalashnikov da aka fi sani da AK-47.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel