Buhari bai kara ko da N1 a kan farashin litar mai ba – Ministan fetur ya karyata PPPRA

Buhari bai kara ko da N1 a kan farashin litar mai ba – Ministan fetur ya karyata PPPRA

- Ministan harkokin man ya fito ya musanya rahoton karin farashin man fetur

- Timipre Sylva ya ce Ma’aikatar tarayya ba ta amince da wani canjin farashi ba

- Sylva ya bada umarni a cigaba da saida mai a kan N160-165 a duk gidajen mai

Jaridar Guardian ta rahoto karamin Ministan harkokin man Najeriya, Timipre Sylva, ya ce babu wani kari da aka yi wa farashin litar man fetur.

Mista Timipre Sylva ya ce farashin man fetur ba zai canza ba har sai zuwa lokacin da gwamnati ta kammala tattauna wa da kungiyoyin kwadago.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar da ke kula da farashin mai watau PPPRA ta bada sanarwar cewa an samu sauyi a kan kudin fetur a watan nan.

Timipre Sylva ya yi kira ga al’umma su yi fatali da rahotannin karin farashin lita zuwa N212.

KU KARANTA: Za a koma saida litar man fetur a kan N212 - PPRPA

“Ko daga ina wannan bayani ya fito, ina so in tabbatar wa ‘Yan Najeriya cewa ko kadan ba gaskiya ba ne.” Sylva ya bayyana wannan a ranar Juma’a.

“Shugaban kasa wanda shi ne Ministan mai, da ni da na ke mataimakinsa na karamin Minista duk ba mu amince da karin kudin fetur koda da N1 ba.”

Ministan ya ce: “Saboda haka ina kira gare ku, ku yi watsi da wannan labari mai karkatar wa.”

A cewar Ministan, gwamnatin tarayya ta na tattauna wa da shugabannin kwadago domin gano yadda za a fuskanci tsadar danyen mai da ake samu.

KU KARANTA: Ba mu yi karin kudin mai ba - NNPC

Buhari bai kara ko da N1 a kan farashin litar mai ba – Ministan fetur ya karyata PPPRA
Karamin Ministan fetur Hoto: Timipre Sylva
Asali: Twitter

“Ina so in kuma tabbatar maku da cewa za a cigaba da zama da masu ruwa da tsaki da ‘yan kwadago har sai an daidaita a kan farashin da ya dace.”

Ya ce: “Zuwa wannan lokaci, ana kira ga ‘yan kasuwa su cigaba da saida fetur a kan farashin da aka sani kafin zuwan wannan sanarwa mai ban takaici.”

Dazu nan Janar Babagana Monguno mai ritaya ya bayyana cewa wasu kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya bada a sayo makamai sun yi kafa.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaron ya ce babu kudi, babu kayan yaki duk da biliyoyin da aka ba tsofaffin hafsoshin sojoji su sayo makamai.

A cewar NSA ba a san inda kudin makaman su ka shiga ba, kuma ba a iya ganin wasu kayan yaki ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel