Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS

Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS

- Hukumar kididdiga ta kasa, NBS, ta ce adadin wadanda ba su da aikin yi a Nigeria ya kai miliyan 23.18

- Hakan na kunshe ne cikin rahoton watanni hudu na karshen shekarar 2020 da hukumar ta fitar

- Jihohin da suka fi yawan marasa ayyukan yi sune Imo, Adamawa da jihar Cross Rivers

'Yan Nigeria miliyan 23.18 ba su yin aikin komai ko kuma suna aiki na kasa da awanni 20 a kowanne mako, wadda hakan ke nufin ba su da ayyukan yi yayin watanni hudu (Q4) na karshen shekarar 2020, rahoton The Cable.

A cewar rahoton na Q4 kan rashin ayyukan yi da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a ranar Litinin, hakan na nufin kashi 33.3 na cikin 100 na masu neman aiki a Nigeria ba su da ayyukan yi a Q4 2020 daga kashi 27.1 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2020.

Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS
Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS
Asali: Original

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: Mutane 3 ake kashewa a Kaduna a kowanne rana cikin shekarar 2020

A lokacin, duk da cewa rashin aikin yi ya ragu daga kashi 28.6 zuwa 22.8 cikin 100, alkalluman rashin aikin yi da rashin samun kwakwarar aikin yi ya kai kashi 56.1 cikin 100.

"A bangaren rashin aikin yi, jihar Imo ce ke kan gaba da kashi 56.64. Mai biye mata ita ce jihar Adamawa da kashi 54.89 dai Cross Rivers da kashi 53.65 cikin 100. Jihohi mafi karancin rashin aikin yi sune Osun, Benue da Zamfara masu alkalluma 11.65, 11.98 da 12.99 kamar yadda aka jero su.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula

"A bangaren rashin kwakwarar aikin yi, jihar Benue ce ke kan gaba da kashi 43.52 cikin 100, masu biye mata kuma sune jihohin Zamfara da Jigawa da 41.73 da 41.29 cikin 100 kamar yadda aka jero su," in ji rahoton.

"Idan an gwamutsa rashin aikin yi da rashin kwararran ayyukan yi, jihohin da ke kan gaba sune Imo da kashi 82.5 cikin 100, sai Jigawa da kashi 80 cikin 100. Mafi karanci kuma sune Ogun da Sokoto da kashi 26.2 da 33.7 cikin 100 kamar yadda aka jero su."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164