Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 41, sun ceto mutum 60 a Borno
- Dakarun sojojin Nigeria sun samu babban nasara a kan yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a Borno
- Sojojin a karamar hukumar Gamboru Ngala sun kashe yan ta'adda 41 sun kuma ceto mutane 60
- Har wa yau, sojojin sun yi nasarar kwato muggan makamai da wasu kayayaki da suka hada da babur, keken dinki da sauransu
Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta sun ceto mutane 60 ciki har da tsofaffi da mata da yara da yan ta'addan kumgiyar Boko Haram suka sace a karamar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.
Sojojin sun kuma kashe a kalla yan ta'adda guda 41 yayin harin da suka kai musu.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya miliyan 23 ba su da ayyukan yi, in ji NBS
Direktan sashin hulda da jama'a na rundunar, Brig Janar Mohammed Yerima ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin rundunar na Twitter inda ya ce sojojin sun kuma kwato makamai bayan kashe yan ta'addan.
"A cigaba da yakin da ake yi da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, dakarun OPERATION LAFIYA ta yi wa ta'adda mugun illa a safiyar yau Litinin 15 ga watan Maris na 2021.
"Dakarun sojojin sun kai sumame a hanyar Gulwa da Musuri da ke karamar hukumar Ngala da ke jihar Borno.
"A Musuri, sojojin sun yi arangama da yan ta'addan suka fafata na kimanin mintuna 45.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula
"Daga bisani sojojin sunyi galaba a kan yan ta'addan suka kashe 41. Sun kuma kwato muggan makamai tare da ceto mutane 60 cikinsu da tsofaffi, mata da yara da yan ta'addan ke tsare da su.
"Kayayakin da aka kwato sun hada da AK-47 guda 12, Bindiga kirar Fabric Nationale guda 8, babur daya, kekuna 6, akwatin gyara na kanikawa, keken dinki, batiri na hada abin fashewa, kayan kara karfin maza da sauransu."
Sanarwar ta ce babban hafsan sojojin kasa, Laftanant Janar Ibrahim Attahiru tuni ya taya sojojin murnar nasarar da suka samu ya kuma bukaci su cigaba da jajircewa.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng