Fetur ya tashi a wasu wurare, farashin ya haura N220 duk da Gwamnati ta ce kudi bai canza ba

Fetur ya tashi a wasu wurare, farashin ya haura N220 duk da Gwamnati ta ce kudi bai canza ba

- Jama’a sun koka da cewa man fetur ya tashi a garin Nsukka, jihar Enugu

- A wasu gidajen mai, abin da ake saida litar fetur ya kai N225 a yau dinnan

- Ana zargin sanarwar da PPPRA ta fitar dazu ne ya jawo farashi ya birkice

Wasu mazaunan garin Nsukka a karamar hukumar Nsukka, jihar Enugu, sun nuna damu wa a game da tashin da farashin man fetur ya yi a yau dinnan.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ana saida litar fetur tsakanin N220 da N225 a gidajen mai a garin Nsukka, bayan sanarwar da aka yi a safiyar yau.

Mazauna wannan gari sun yi hira da hukumar dillacin labarai na kasa, NAN inda su ka tabbatar da cewa wasu gidajen mai da yawa sun ki fito wa aiki.

Wani babban malamin ilmin siyasa a jami’ar Nsukka ta UNN, Ifeanyichukwu Abada, ya ce abin bai yi masa dadi ba, da ya je ya na sayen litar fetur a N225.

KU KARANTA: PPPRA ta shafe bayanin karin kudin fetur a watan Maris

“Gidajen mai da-dama a Nsukka ba su saida fetur, hakan ya sa mai ya yi wahala, sauran wadanda su ke saida wa, su ka zabi farashin da su ka ga dama.”

Abada ya ce tashin farashin bai rasa nasaba da sanarwar da PPPRA ta yi, kafin a musanya rahoton.

Shi kuma wani lauya mai suna Chidi Onah, ya ce karin kudin man fetur ya zama jikin ‘yan Najeriya, ya ce duk wata sai an ji labarin sabon farashi.

Onah esq ya ce: “Na saye lita yau da safen nan a gidan mai a kan N223. Na shafe mintuna fiye da 45 a layi saboda gidajen mai kadan ne su ke saida fetur.”

KU KARANTA: Farashin man fetur zai haura N210 a gidajen mai - PPPRA

Fetur ya tashi a wasu wurare, farashin ya haura N220 duk da Gwamnati ta ce kudi bai canza ba
Gidan mai a Legas, 2011. Hoto: Getty/PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Irin su Onah su na ganin kungiyar kwadago ba ta yin abin da ya kamata wajen kare hakkin ‘yan Najeriya, ya ce an bar gwamnati ta na galabaitar da jama’a.

Wani Bawan Allah da ke zaune a Arewacin Najeriya ya bayyana cewa duk da sanarwar da aka yi, sai da ya saye man fetur a kan N212 a ranar Juma’a da rana.

Dazu ne aka fahimci cewa gwamnatin tarayya ta yi amai ta lashe, ta ce babu batun kara kudin mai sai an gama tattaunawa da shugabannin 'yan kwadago.

Timipre Sylva ya musanya sanarwar da hukumar PPPRA ta yi a baya, ya ce ce ba za ayi karin kudin fetur ba har sai an karkare zaman da ake yi da kwadago.

A cewar Timipre Sylva, Muhammadu Buhari bai kara ko da N1 a kan farashin litar mai ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng