Barazana ga rayuwa: Sheikh Abdallah Pakistan ya kai karan Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu

Barazana ga rayuwa: Sheikh Abdallah Pakistan ya kai karan Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu

- Kuma dai! An sake shigar da Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu

- Da alamun an samu sabani tsakaninsa da wani babban Malami, Farfesa Abdullahi Pakistan

Wata kotun majistare a jihar Kano ranar Juma'a ta umurci kwamishanan yan sandan jihar ya gudanar da bincike kan zargin barazana da suka da aka daurawa Sheikh Abduljabbar Kabara.

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya bada wannan umurni ne bayan sauraron karan da Abdulrahman Nasir, lauyan Sheikh Abdallah Pakistan ya shigar, rahoton NAN.

Umurnin mai lamba KA/CMC14/003/2021, ta bukaci kwamishanan yan sandan ya gabatar da sakamakon bincike gaban kotu daga yanzu zuwa ranar 27 ga Maris.

DUBA NAN: Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Barazana ga rayuwa: Sheikh Abdallah Pakistan ya kai karan Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu
Barazana ga rayuwa: Sheikh Abdallah Pakistan ya kai karan Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Za ku tuna cewa ranar 3 ga Febrairu, gwamnatin jihar Kano ta dakatad da Sheikh Abduljabbar daga wa'azi kuma ta kulle Masallacinsa.

Bayan haka gwamnatin jihar a ranar 7 ga Febrairu ta sanar da cewa za ta shirya mukabala tsakanin Kabara da sauran Malaman Kano cikin makonni biyu.

Bayan makonnin biyu gwamnatin ta shirya mukabala ranar Lahadi, 7 ga Maris 2021.

Amma ana sauran yan kwanaki, kungiyar Jama'atu a jawabin da ta saki tace babu bukatar mukabala da AbdulJabbar, saboda haka ba ta goyon bayan zaman.

Ana jajibirin mukabalar, kotun majistare ta dakatad da mukabalar har zuwa ranar 22 ga Maris domin sauraron karar.

A bangare guda, tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya zama jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

An yi wannan nadi ne a babban taron Maulidin da ke gudana a jihar Sakkwato.

Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagorancin bikin nada Sanusi.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng