Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta kunshi majalisar wakilai da na dattijai.

Yayinda majalisar dattijai ke da mambobi 109, majalisar wakilai na da mambobi 360.

Tun da Najeriya ta koma tsarin demokradiyya a 1999, mata na kukan ba'a damawa da su a harkar majalisa.

Hakan ya sa yanzu suke bukatar a basu wani kaso na musamman na mambobi.

Jawabi kan haka, wata mambar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ayedaade/Irewole/Isokan a jihar Osun, Taiwo Ulukemi Oluga, tace ba zasu amince a cigaba da mayar da su saniyar ware ba.

Saboda haka suna bukatar a baiwa mace kujerar Sanata daya a kowace jiha.

DUBA NAN: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu
Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu
Asali: UGC

DUBA NAN: Yayin kokarin cetosu an raunata wasu dalibai, har yanzu ana neman 30: Gwamnatin jihar Kaduna

Ta ce mata 19 kadai cikin 469 ke majalisa.

Saboda haka, Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen mata dake majalisar dattawa da wakilai yanzu.

Na majalisar wakilai:

1. Taiwo Oluga – Ayedaade /Irewole/Isokan (Osun-APC)

2. Tolulope Tiwalola Akande-Sadipe – Oluyole (oyo-APC)

3. Khadija Bukar Abba Ibrahim - Damaturu / Gujba / Gulani /Tarmuwa (Yobe-APC)

4. Boma Goodhead - Akuku Toru / Asari Toru (Rivers-PDP)

5. Beni Butmak Lar - Langtang North / Langtang (Plateau-PDP)

6. Onanuga Adewunmi Oriyomi - Ikenne/Shagamu/Remo North (Ogun-APC))

7. Aishatu Jibril Dukku - Dukku / Nafada (Gombe-APC)

8. Ogunlola Omowumi Olubunmi - Ijero / Ekiti West / Efon (Ekiti-APC)

9. Zainab Gimba - Bama / Ngala / Kala – Balge (Borno-APC)

10. Onuh Onyeche Blessing - Otukpo / Ohimini (Benue-APGA)

11. Lynda Chuba Ikpeazu - Onitsha North / Onitsha South (Anambra-PDP)

12. Nkeiruka C. Onyejeocha - Isuikwuato / Umuneochi (Abia-APC)

Na majalisar dattawa:

1. Stella Oduah - Anambra North (Anambra -PDP)

2. Rose Oko – Cross River North (Cross River -PDP)

3. Oluremi Tinubu – Lagos Central (Lagos-APC)

4. Aishatu Dairu – Adamawa Central (Adamawa-APC)

5. Uche Ekwunife – Anambra Central (Anambra-PDP)

6. Betty Apiafi – Rivers West (Rivers PDP)

7. Akon Eyakenyi – Akwa-Ibom South (Akwa-Ibom-PDP)

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng