Ina nan a kan bakata: Jami’an tsaro su bindige duk wanda aka samu dauke da AK-47 inji Buhari

Ina nan a kan bakata: Jami’an tsaro su bindige duk wanda aka samu dauke da AK-47 inji Buhari

- Muhammadu Buhari ya na nan a kan bakarsa a kan masu rike bindigogi

- Shugaban kasar ya ce a harbe duk wani wanda aka gani ya dauki AK-47

- Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya yi zama da Sarakunan Najeriya

Fadar shugaban kasa ta fito ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada umarninsa na ganin bayan manyan masu laifi, wadanda su ka addabi Najeriya.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Maris, 2020, shugaban kasar ya kara tabbatar da cewa jami’an tsaro su harbe duk wani wanda aka samu dauke da bindigar AK-47.

Femi Adesina ya rahoto shugaban kasar ya na mai hakikance wa a kan matakin da ya dauka a kan miyagun da su ke rike makamai ba tare da mallakar izini ba.

Muhammadu Buhari ya yi wannan magana ne sa’ilin da ya yi wani zama da majalisar sarakunan gargajiya a fadar shugaban kasa na Aso Villa a birnin tarayya.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Mun shirya ba Najeriya agaji - Amurka

Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabi da taken cewa “Za mu dura kan masu laifi da kyau, shugaba Buhari ya fada wa sarakunan gargajiya.”

Adesina ya ce shugaban Najeriyar ya sake bada umarnin a harbe masu rike bindigar AK-47.

Shugaban kasar ya na magana ne a kan miyagun ‘yan bindigan da ‘yan ta’addan da su ke yawo da shahararriyar bindigar nan ta AK-47 a fadin jihohin Najeriya.

“Abin da ke ba ni mamaki shi ne abin da ke auku wa a Arewa maso yamma, mutane iri daya ke kashe juna, su ke tsere wa da dabbobinsu, su na kona gari.” inji Buhari.

KU KARANTA: Hafsun Sojojin Najeriya sun dura jihar Oyo

Ina nan a kan bakata: Jami’an tsaro su bindige duk wanda aka samu dauke da AK-47 inji Buhari
Buhari da sarakunan gargajiya
Asali: Twitter

Idan za ku tuna Mai alfarma Sultan Muhammad Abubakar III da mai martaba Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi su ka jagoranci Sarakunan zuwa Aso Villa.

Jami’an gwamnati da su ka halarci taron sun hada da hafsoshin tsaro, Babagana Monguno, IGP Mohammed Adamu; Darektan DSS da NIA, Yusuf Bichi, Ahmed Abubakar.

Igwe Nnaemeka Achebe; Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar; Jajan Opobo, Dr. Dandeson Douglas Jaja; Dr, Rilwanu Suleiman Adamu; Alhaji Muhammad Iliyasu; Alawen Ilawe-Ekiti, Oba Adebanji Ajibade Alabi sun samu zuwa wannan taro da aka yi a jiya da rana.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng