Yanzu-yanzu: Hukumar PPPRA ta goge sanarwar da tayi na karin farashin mai

Yanzu-yanzu: Hukumar PPPRA ta goge sanarwar da tayi na karin farashin mai

- Kamfanin NNPC ya yi fashin baki kan rahotannin kara farashin man fetur

- Hankulan yan Najeriya sun tashi yayinda suka wayi gari da labarin tashin farashin

- Da wuri PPPRA ta cire sanarwan daga shafinta na yanar gizo

Hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan arzikin mai a Najeriya ta goge sanarwar da tayi a shafinta na yanar gizo na karin farashin litan man fetur a Najeriya.

Hukuma ta sanar da kara farashin a shafinta a daren Alhamis, amma ta goge da safiyar Juma'a sakamakon kalaman jama'a.

Wannan ya biyo bayan jawabin Kamfanin man feturin Najeriya NNPC inda ya sake jaddada cewa ba za a kara farashin litan man fetur a watan Maris ba duk da tashin da farashin danyen man yayi a kasuwar duniya.

DUBA NAN: Jerin tsaffin gwamnoni 7 da aka jefa gidan yari

Yanzu-yanzu: Hukumar PPPRA ta goge sanarwar da tayi na karin farashin mai
Yanzu-yanzu: Hukumar PPPRA ta goge sanarwar da tayi na karin farashin mai
Asali: Original

DUBA NAN:Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10

Da safiyar Juma'a, hukumar PPPRA ta yi lissafin yadda farashin litar PMS wanda aka fi sani da man fetur ya kamata ya kasance.

Hukumar ta bayyana wannan karin kudi ne a ranar 12 ga watan Maris, 2021 a shafinta na yanar gizo.

An yi lissafin ne a kan yadda ake shigo da kaya.

Wannan sauya-sauye da aka samu ya na nufin cewa litar fetur zai kara kudi a gidan mai. Idan aka tara duka wadannan kudi, za a saida fetur a gidan mai a kan N212.

Hakan ya tada hankalin jama'a inda jam'iyyar adawa ta PDP tayi Alla-wadai da wannan abu da gwamnatin shugaba Buhari tayi.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel