Jerin tsaffin gwamnoni 7 da aka jefa gidan yari

Jerin tsaffin gwamnoni 7 da aka jefa gidan yari

Lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ofis a shekarar 2015, ya bayyana cewa zai yi yaki da cin hanci da rashawa.

Tsakanin 2015 da ya hau mulki zuwa yanzu, wasu tsaffin gwamnoni kuma mambobin jam'iyyar APC sun shiga gidan yari.

Legit.ng ta kawo muku jerin gwamnoni bakwai da suka ci gidan kurkuku a Najeriya"

1. Orji Uzor Kalu Kalu: tsohon gwamnan jihar Abiya zai kwahse shekaru 12 kan laifin almundahanar N7.65 billion lokacin yake gwamna tsakanin shekarar 1999 da 2007. A yanzu haka Sanata ne kuma daya daga cikin shugabannin majalisa.

2. Joshua Dariye Dariye: Tsohon gwamnan jihar Plateau ya shiga gidan yari tun 2018 kuma zai kwashe shekaru 14 kan laifin facaka da bilyan 1.162. An rage yawan shekarun zuwa 10.

3. Jolly Nyame: Tsohon gwamnan jihar Taraba ya shiga gidan yari tun 2018 kuma zai kwahs shekaru 14 kan laifin karkatar da kudin baitul mali lokacin da yake gwamnan jihar.

4. James Bala Ngilari Ngilari, tsohon gwamnan jihar Adamawa wanda aka jefa gidan yari a 2017 kuma zai kwashe shekaru 5 kan laifin almundahanar N167 million.

5. Lucky Igbinedion Igbinedion, tsohon gwamnan jihar Edo ya kwashe watanni shida a gidan yari a shekarar 2008.

6.James Ibori Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta wanda kotun Ingila ta yankewa hukuncin shekaru 13 a gidan yari kan almundahanar $250 million. Ya kammala wa'adinsa kuma ya dawo Najeriya.

7. Late Diepreye Alamieyesegha Alamieyesegha, tsohon gwamnan jihar Bayelsa wanda yayi rib da ciki da bilyan 3.7 na jiharsa kuma ya kwashe shekaru 2 a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel