Manyan kusoshin Jam’iyyar PDP sun fara yin zaman gaggawa a Abuja a kan '2023' tun yanzu

Manyan kusoshin Jam’iyyar PDP sun fara yin zaman gaggawa a Abuja a kan '2023' tun yanzu

- Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara shirya hanyar da za ta kai ga nasara a 2023

- Majalisar BOT ta yi zama a Abuja domin duba inda jam’iyyar ta saka gaba

- Sanata Adolphus Wabara ya fitar da jawabi bayan an yi wannan taro a jiya

Rahotanni sun zo mana cewa majalisar amintattu ta jam’iyyar hamayya ta PDP, ta shirya wani taron gaggawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Maris, 2021.

Jaridar Daily Trust ta ce an shirya wannan taro na musamman ne da nufin a yi waje da jam’iyyar APC daga kan mulkin kasar nan a zabe mai zuwa na 2023.

Kamar yadda bayanan bayan taron da sakataren BOT, Sanata Adolphus Wabara ya fitar su ka nuna, zaben 2023 ne makasudin wannan zaman da aka yi.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce akwai bukatar majalisar amintattu ta jam’iyyar PDP ta zauna a sakamakon halin tashin-tashinan da aka shiga a kasar.

KU KARANTA: Kotu ta tsige shugabannin PDP a Ebonyi bayan rikicin cikin-gida

Rahoton ya bayyana cewa ‘Yan majalisar BOT sun duba nasarorin da aka samu wajen shawo kan fitattun jiga-jigan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da su ka samu sabani.

Majalisar ta ce za ta tuntubi gwamnoni kafin a san matakin da za a dauka domin kara dinke baraka.

BOT ta sha alwashin cewa ba za ta bari a lalata alakar da ke tsakanin ‘ya ‘yan gidan jam’iyyar hamayyar ba, musamman shugabannin da ke kula da jam’iyyar.

Jawabin ya ce: “A shirye majalisar nan ta ke domin tabbatar da komai ya dawo daidai, an samu zaman lafiya a duka bangarorin jam’iyya, domin a samu cigaba.”

KU KARANTA: Amaechi ya yi martani bayan Wike ya ce Buhari ke yi masa shinge

Manyan kusoshin Jam’iyyar PDP sun yi zaman gaggawa a Abuja a kan '2023' tun yanzu
Shugaban PDP na kasa Prince Uche Secondus, Hoto: @OfficialPDPNigeria
Asali: Twitter

Sanata Adolphus Wabara da sauran ‘yan majalisar su ka ce sai jam’iyya ta zauna lafiya kalau ne za a iya dabbaka manufofi, a cin ma muradun da aka sa a gaba.

Bayan shafe shekaru 16 a kan mulki, PDP ta rasa gwamnati a zaben 2015 inda Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya doke shugaba Goodluck Ebele Jonathan.

A watan jiya kun ji labarin yadda shugabannin jam'iyyar PDP su ka samu damar gana wa da tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya).

A ranar Juma'a 19 ga watan Fabrairu shugabannin PDP su ka yi zama da IBB a gidansa da ke Minna a kokarin dinke barakar cikin gida kafin zuwan zaben 2023.

An yi wannan zama ne a karkashin shugabancin tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel