Kyakkyawar 'yar Arewa ta ciri tuta a Ingila, ta samu babban lambar yabo

Kyakkyawar 'yar Arewa ta ciri tuta a Ingila, ta samu babban lambar yabo

- Wata budurwa mai suna Maryam Muhammed ta ciri tuta a kasar Birtaniya

- Kyakkayawar budurwar ta samu mumtaz bayan kammala karatun zama lauya kuma ta samu lambar yabon shugaban makarantar

- Jam'iyyar APC, shiyar Birtaniya ta bayyana hakan a shafinta na kafar sada zumunta

Wata budurwa yar Najeriya mai suna Maryam Muhammed wacce ta kammala karatun zama lauya a Birtaniya ta samu lambar yabon shugaban makarantar.

A cewar APC United Kingdom, budurwar ta kammala karatu a jami'ar Queen Mary University of London.

Kyakkyawar 'yar Arewa ta ciri tuta a Ingila, ta samu babban lambar yabo
Kyakkyawar 'yar Arewa ta ciri tuta a Ingila, ta samu babban lambar yabo Credit: APC United Kingdom
Source: Facebook

DUBA NAN: Tirƙashi: Majilisar wakilai tace kuɗin da Burtaniya suka dawo dasu na jihar Delta ne

Jawabin APC UK ya bayyana cewa: Jarumar yar Najeriya, Maryam Muhammed ta samu matsayin mumtaz a karatun lauya daga jami'ar Queen Mary University of London kuma ta samu lambar yabon shugaban makarantar bisa kokarinta."

DUBA NAN: Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina

A wani labarin kuwa, matar wani manomi, Funmilayo Oluwadara, ta haifi 'yan hudu a karamar hukumar Ogbomoso ta Arewa na jihar Oyo.

Matar mai shekaru 38 ta haifi mata hudu da na miji daya a asibitin Ayoka Clinic and Maternity Center, Oke Ado, Ogbomosho a ranar Alhamis 4 ga watan Maris.

Mrs Oluwadara, mazauniyar kauyen Ahoroka a garin Oyo, yanzu tana da yara 10 duba da cewa tana da yara biyar kafin ta haifi yan biyar din.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel