Rayuwar aure: Dalilai 6 da su ka jawo Matan yau suka rabu da Yara, su ke yin wuf da Dattawa
Samari da-dama su na kukan ‘yan matan wannan zamanin sun buge da auren maza masu yawan shekaru, yayin da su kuma su ke fama da gwauranta.
Jaridar Daily Trust ta yi bincike a game da abin da ya jawo tsofaffi su ke yawon cin kasuwa a yau.
Wata Buduwar mai shekara 26 ta karkada mabudin mota kirar Venza, ta ce maigidanta ya ba ta kyauta, duk da ya na da shekaru, ya na kashe mata kudi.
Wannan mata ta ce ta na tare da matashin saurayinta na tsawon shekaru ana soyayya, amma bai da ikon halinta, don haka da dattijo ya zo, ta yi wuf da shi.
Daga cikin dalilan da su ka sa ake auren manyan maza akwai:
KU KARANTA: Amarya ta birkice ranar biki, ta gano Ango ya na da aure
1. Dukiya
Tsofaffin mazan nan sun fi mafi yawancin samari arziki, don haka mace za ta more idan ta shiga gidansu. Wadannan maza sun riga sun tara kudin da ake bukata.
2. Sanin hannu
Wata Baiwar Allah ‘yar shekara 28 ta ce dattawa sun fi sanin rayuwa; sun ga yau da gobe. Hakan na nufin cewa wadannan maza sun fi ‘yan bana-bakwai basira.
3. Mu’amala
Ana ganin cewa tsofaffin maza sun fi saukin mu’amala a rayuwa. Manyan mutane su kan saurari mata, kuma ba su da saurin fushi, ga su da yawan lallabar mata.
4. Ruwan ido
Samari sun cika ruwan ido da kwadayi, a gefe guda kuwa, wata budurwa ta ce tsofaffin maza ba su cika maida hankali a kan dirin ‘yan mata kamar yaran yanzu ba.
KU KARANTA: Al'adun gargajiya da ake yi a bikin aure a kasar Sudan
5. Takara
Babban mutum bai da wani lokacin da zai rika kokarin takara da mace, ya riga ya yi mata nisa, don haka ba zai rika kokarin dakile hanyar samu da cigabanta ba.
6. Kula
‘Yan mata su na zaben masu iyali ne saboda a cewar wata daga cikinsu, irin wadannan maza sun fi kula da mace kamar kwai, sun fi bada hakkin aure fiye da samari.
A 'yan kwanakin nan, labarin wani matashi mai suna Babangida Sadiq Adamu da ya shirya auren mata biyu a rana daya ya karada shaukan sada zumunta na zamani.
Yanzu dai tuni Adamu ya auri Malama Maimuna Mahmud tare da wata sahibarsa mai suna Maryam a ranar 6 ga watan Maris 2021 a wani masallaci da ke Abuja.
Babangida Sadiq Adamu ya ara hadu wa ne da Maryam, daga baya kuma ya ga Maimuna.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng