Amarya ta birkice ranar biki bayan gano sahibinta na da aure kuma Iyalansa na bogi ne

Amarya ta birkice ranar biki bayan gano sahibinta na da aure kuma Iyalansa na bogi ne

- Murna ta gagari wata amarya a ranar bikinta bayan ta gano cewa angonta ya na da aure har da 'ya'ya da wata matar

- Bayan boye mata gaskiya a kan iyalinsa, angon ya dauko hayar mutane a matsayin danginsa

- Ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun ce amaryar ta zargi kanta saboda ba ta yi bincike ba kafin aure

Wata Amarya ta shiga ruɗani da bata taɓa shiga bayan ta gano wanda ta angonce da shi zuƙi ta malle yayi don kawai ya aureta ana tsaka da bikinsu.

Acewar wata mai amfani da shafin sadarwa na Tuwita (@iam_liliane) wacce ta yi iƙirarin halartar bikin tace;

"Angon nata yana da aure har da ƴa'ƴa amma bai taɓa shaida mata ba har sai da ta gano a ranar bikin."

Ta ƙara bayyana cewa "mijin nata ya yi hayar dangin bogi don su tsaya masa a matsayin ahalinsa a wurin bikin kamu da na coci.

Ta rubuta kamar haka "Bikin da na halarta jiya, yanzu nake sanin angon ya na da aure kuma hayar mutane ya yi don su tsaya a matsayin ahalinsa a bikin kamu da coci."

Amaryar ta birkice ranar biki bayan gano sahibinta na da aure kuma Iyalansa na bogi ne
Amaryar ta birkice ranar biki bayan gano sahibinta na da aure kuma Iyalansa na bogi ne
Source: Twitter

"Wannan yaudara haka!! Amarya ta ruɗe, kuma ta rasa abin yi. An yaudare ta, ashe duk bogi ce".

Sai dai rubutun na ta ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta inda wasu ke sukar amaryar bisa rashin bin diddigi, ta ƙasa, ta binciki angon kafin ranar bikin nasu.

A kwanakin baya Legit.ng Hausa ta rawaito yadda wani magidanci ya saka kaifin fikar hakoransa ya gartsawa matarsa cizo har ta kai ga ya guntule mata yatsu uku.

Sa dai, magidancin ya shiga hannun jami'an tsaro kuma sun gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.

Magidancin ya amsa laifinsa a gaban kotu tare da neman sassauci a hukuncin da Alkali zai zartar

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel