Sojoji sun karbe manya-manyan makamai bayan sun kashe na kashewa a Sojojin Boko Haram

Sojoji sun karbe manya-manyan makamai bayan sun kashe na kashewa a Sojojin Boko Haram

- Sojojin kasa sun yi galaba a kan ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP

- Dakarun Najeriya sun kashe Sojojin ta’adda a Chikun Gudu da Kerenoa

- An karbe makamai da kayan yakin da ‘Yan ta’addan ke amfani da su

Dakarun sojojin kasa na Operation Tura ta kai bango sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a hare-haren da su ka kai a jihar Borno.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin rundunar, sojojin na Operation Tura Ta kai bango sun kai wa ‘yan ta’addan hari a yankunan Chikun Gudu da Kerenoa.

A jawabin da Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Laraba a garin Abuja, ya ce wadannan kauyuka su na karkashin karamar hukumar Marte.

A ranar Talata sojojin Operation Lafiya Dole da wasu dakaru daga bataliyar 402 su ka hada-kai da Operation Tura Ta kai bango, su ka auka wa ‘yan ta’addan.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun tsere da mutum sama da 100 a Zamfara

Bayan hallaka ‘yan ta’adda har 25, dakarun sojojin kasan Operation Tura Ta kai bango sun karbe makamai daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Daga cikin makaman da aka iya karbe wa akwai katuwar bindiga mai lugude ta Browny Machine Gun, da bindigogin AK-47 20, da wasu kananan bindigogi biyar.

Bayan haka an karbe makamin 'Mortar Tube; daya da manyan bindigogi masu barin wuta a harin.

“Sauran makaman da aka karbe daga harin su ne; makami mai baro jirgin sama uku, da bindigogin Grenade Launchers biyu, da bindigogin kan mota biyu.

KU KARANTA: Sojoji sun yi raga-raga da Boko Haram a Marte

Sojoji sun karbe manya-manyan makamai bayan sun kashe na kashewa a Sojojin Boko Haram
Motar yakin Boko Haram Hoto: @HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Babban jami’in hulda da jama’a da yada labarai na sojojin kasa, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya ce dakarun kasar sun yi gaba da motar Hilux ta CJTF.

Janar Yerima ya ce shugaban hafsun sojojin kasa, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru, ya yabi aikin da sojojin na sa su ka yi, ya yi kira a gare su da su cigaba da kokari.

Kwanaki ne aka ji Ministan yada labaran da al'adu na tarayya, Alhaji Lai Mohammed ya soki yadda wasu mutanen Najeriya ke kallon al'amuran tsaro a kasar nan.

Lai Mohammed ya bayyana irin abin da gwamnatin APC ke yi don ganin ta ceto dalibar makarantar nan da 'yan Boko Haram su ka sace a Dapchi, Leah Sharibu.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel