Sarkin Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata fiye da 100 a makon da ya wuce ba a sani ba

Sarkin Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata fiye da 100 a makon da ya wuce ba a sani ba

- Sarkin Anka ya ce an sace mutane fiye da 100 a jihar Zamfara a makon jiya

- ‘Yan bindiga sun sace masu hake-haken ma’adanai a yankin Anka da Maru

- Attahiru Ahmad ya ce hakan ya faru ne lokacin da aka sace yara a Jangebe

Mai martaba Sarkin Anka a jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya ce masu hakar ma’adanai fiye da 100 aka sace tsakanin garin Anka da Maru kwanakin baya.

Alhaji Attahiru Ahmad ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun tsere da wadannan mutane ne a lokacin da su ka kawo masu hari a ranar 2 ga watan Maris, 2021.

Shugaban majalisar Sarakunan na Zamfara ya yi wannan bayani ne a garin Gusau, a lokacin da Janar Lucky Irabor ya jagoranci hafsoshin sojoji zuwa jihar.

NAN ta rahoto Sarkin ya na cewa wannan abu ya auku ne a lokacin da hankalin gwamnati ya karkata wajen ceto ‘daliban makarantar Jangebe da aka sace.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya fallasa wadanda su ka sace Yaran GGSS Jangebe

Mai martaba Attahiru Ahmad ya kara da cewa an kashe mutane 10 a lokacin da ‘yan bindigan su ka auka wa wani wuri da ake aikin hake-hake a jihar Zamfara.

Sarkin Anka, Ahmed ya ke cewa: “’Miyagun ‘yan bindigan su na ta kai wa wadannan masu aikin hako ma’adanai hari, su na tsere wa da kudinsu da dukiyoyinsu."

Sarkin ya yi bayanin alakar masu aikin hako ma’adanai da ‘yan bindigan jihar, ya ce sun yi mamakin jin an hana jirgin sama tashi a Zamfara da ba ta filin jirgi.

A cewar Alhaji Attahiru Ahmad, idan gwamnati za ta sa wannan doka, ya kamata ta shafi sauran jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaron da ta fi na Zamfara.

KU KARANTA: Sarkin Anka da aka tsige ya kai IGP, wasu zuwa kotu

Sarkin Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata fiye da 100 a makon da ya wuce ba a sani ba
Shugabannin sojoji a jihar Zamfara
Asali: Twitter

Ya ce: “Masu hako ma’adananmu wadanda aka ba su lasisi, su na taimaka wa cigaban tattalin arzikinmu, kuma su na tallafa wa wadanda ke sansanin gudun hijira.”

A jawabin na sa, Sarkin Anka ya nuna ya na goyon bayan sulhu da 'yan bindiga, ya ce an samu zaman lafiya a sakamakon sasanta wa da gwamnatin jiha ta yi da miyagu.

A makonnin baya kun ji cewa Gwamnan jihar Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji domin ceto daliban makarantar Jangebe da aka sace.

Auwalu Daudawa shi ne 'dan bindigan da ya jagoranci satar daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara wanda aka yi a jihar Katsina a watannin da su ka wuce.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel