Har yanzu bamu samu kudin fara aikin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kaduna ba – Amaechi

Har yanzu bamu samu kudin fara aikin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kaduna ba – Amaechi

Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya bayyana cewa har yanzu Najeriya bata samu bashin kudin daga kasar China ba, wanda da shi take sa ran gudanar da aikin shimfida layin dogo na jirgin kasan Ibadan zuwa Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito gwamnati ta nemi bashin dala biliyan 6.7 daga bankin EXIM na kasar China domin gudanar da wannan muhimmin aiki, yayin da Najeriya za ta bayar da kashi 15 na kudaden aikin.

KU KARANTA: Da yan Najeriya sun zabi Atiku da basu shiga mawuyacin hali ba – Obasanjo

Haka zalika gwamnatin ta shiga yarjejeniya da kamfanin China Civil Engineering Corporation, CCECC don gudanar da aikin a kan dala biliyan 6.68, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ministan ya bayyana haka ne jahar Legas yayin da yake duba aikin jirgin kasa daga Ebutte Metta zuwa Apapa, inda yace gwmanatin Najeriya a shirye take daga bangarenta, amma China bata sakan mata sauran kudaden da ake bukata ba.

Sai dai game da aikin Ebutte Metta zuwa Apapan ma, Ministan ya koka kan yadda aikin yake tafiya, don haka yake ganin ba lallai a kammala shi a cikin watan Mayun 2020, haka zalika ministan ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda kamfanin CCECC take gudanar da aikin.

Daga karshe ministan ya bayyana cewa da zarar kudaden sun samu, zasu cigaba da aikin Ibadan zuwa Kaduna, kuma yana sa ran zasu kammala aikin cikin lokacin da aka tsara. Daga cikin wadanda suka raka ministan har da shugaban kamfanin CCECC Zhao Dianlong.

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa, Sanatan Ahmad Lawan ya musanta zargin da wasu yan Najeriya ke ma majalisar dokokin Najeriya game da cewa ta zama yar amshin shata ga gwamnatin Buhari, ta yadda take baiwa duk bukatun gwamnatin Buhari goyon baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel