'Yan bindiga: Tubabben sarkin Zamfara ya maka IGP da wasu a kotu
-Tsohon sarkin Maru na jihar Zamfara ya maka Sifeta janar na 'yan sanda da wasu mutane 5 a kotu
- Tsohon sarkin ya bukaci Naira Biliyan 6.5 a hannunsu, sakamakon ajiyeshi a hannun su da kuma bata masa suna
- Bayan sauraron karar, Alkalin kotun, Fatima Aminu ta mayar da shari'ar babbar kotu don yanke hukunci
Tsohon sarkin Maru dake jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Ibrahim, ya maka Sifeta Janar na 'yan sanda da wasu mutane 5 akan tsareshi ba bisa ka'ida ba da kuma bata masa suna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta tube wa Ibrahim rawani shekarar da ta wuce, kuma ta adana shi a gidan gwamnati na tsawon watanni 11, sakamakon laifi taimakon 'yan ta'addan da suka addabi jihar.
KU KARANTA: FEC ta amince da N13.08trn na kasafin kudin 2021
KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)
Sauran mutane 5 da Ibrahim ya maka a kotun sune DG na 'yan sanda, CP na 'yan sanda, AD na 'yan sanda, DSS da sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Bala Maru.
Sarkin da ya kai karar kotun tarayya dake Gusau, na neman Naira Biliyan 6.5 a hannun su sakamakon kama shi da suka yi ba bisa ka'ida ba, rike shi na wani lokaci da kuma bata masa suna a idon duniya.
Bayan Alkalin kotun, Fatima Aminu ta gama sauraron karar, ta maida karar babbar kotun jihar Zamfara don yanke hukunci.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni da gwamnoni 'yan uwansa sun jawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum kunne akan ya dinga tsananta tsaro musamman idan zai je wurare masu hadarin gaske, amma sai yace "ya batun mutane na na jihar Borno? Me zai faru dasu?" A wannan halin tashin hankalin dake Borno.
Fayemi yayi wannan maganar ne ranar Laraba yayin da ya jagoranci tafiya tare da gwamnan Sokoto, wanda shine mataimakin shugaban NGF, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shine shugaban gwamnonin APC da kuma Simon Lalong na jihar Plateau, wanda yake shugabantar NGF, zuwa jihar Borno don jajantawa Zulum akan harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng