Gwamnan Zamfara ya fasa-kwai, ya fallasa wadanda su ka sace ‘Yan mata a Jangebe

Gwamnan Zamfara ya fasa-kwai, ya fallasa wadanda su ka sace ‘Yan mata a Jangebe

- Bello Matawalle ya ce ba Fulani kadai su ka sace Daliban GSSS Jangebe ba

- Gwamnan na Zamfara ya ce akwai Hausawa da dama a cikin ‘Yan bindigan

- Akwai wata da ta iya gane fuskar daya daga cikin wadanda su ka dauke su

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi magana a game da wadanda su ka shiga makarantar ‘yan mata su ka sace ‘dalibai a garin Jangebe.

A ranar Laraban nan ne gwamna Bello Matawalle ya bayyana cewa wadanda su ka sace ‘yan matan wannan makaranta, mutanen kabilar Hausa-Fulani ne.

Mai girma gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels Television a shirinsu na siyasa na Politics Today dazu.

Da yake fallasa wadanda su ka yi wannan danyen aiki, Matawalle ya bayyana cewa ba Fulani kadai su ka sace wadannan dalibai kamar yadda ake tunani ba.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun harbe wani matafiyi a jihar Osun

A cewar gwamnan, an samu wata daliba da ta gane mutum guda a cikin ‘yan bindigan, kuma ta yi alkawarin za ta sanar da hukuma duk lokacin da ta yi ido da shi.

“Sun ce mafi yawansu Hausawa ne, wasunsu kuma Fulani ne. Asali ma sai da su ka fada wa ‘yan makarantar su yi masu addu’a.” inji gwamnan na Zamfara.

“Saboda haka sun fito ne daga wurare daban-dabam, akasin tunanin da ake yi na cewa dukansu Fulani ne.”

“’Yan jarida sun yi hira da wasu daga cikin yaran wanda ta gane wani a cikinsu (masu garkuwa da mutanen.”

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun raunata mutum 1, sun kashe mutane a Igabi, Kauru

Gwamnan Zamfara ya fasa-kwai, ya fallasa wadanda su ka sace ‘Yan mata a Jangebe
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle
Asali: Twitter

Wata ta fada mana ta san wani daga cikinsu wanda Bahaushe ne, wanda yake zuwa kasuwar

Rahotanni su na zuwa mana cewa akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa yayin da da dama su ka jikkata a Jangebe, garin da aka sace dalibai mata a jihar Zamfara.

Bayan daliban da aka sace sun kubuta daga hannun yan bindiga, an kai su asibiti domin a duba lafiyarsu, daga nan aka maida su zuwa makarantar da aka sace su.

A ranar Laraba wasu matasa a garin su ka fara kai wa duk wanda ya karaso makarantar 'yan matan hari, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar wani Bawan Allah.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng