Musiba ta aukawa dangi 1 a Kogi, an sace mata 3 da tsakar dare, an ce sai an biya N100m

Musiba ta aukawa dangi 1 a Kogi, an sace mata 3 da tsakar dare, an ce sai an biya N100m

- A jiya ‘Yan bindiga su ka shiga karamar hukumar Koton Karfe sun sace yara uku

- Wadannan Miyagu sun dauke ‘Ya ‘ya mata daga gidan mutum daya a Eteh – Okofi

- An bukaci dangin wadannan ‘Yan mata su biya N100m a matsayin kudin fansarsu

Jiya 'yan bindiga su ka dauke wasu mata ‘yanuwa uku a wani gida a kauyen Eteh – Okofi, a karamar hukumar Koton Karfe da ke jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta yi magana da wani daga cikin ‘yanuwan wadannan yara da aka dauke, ya tabbatar da cewa abin ya faru ne ranar Talata.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, ‘yan bindigan sun duro gidan ne da daidai karfe 12:43 na dare.

Wadannan ‘yan bindiga sun bullo daga daji dauke da manyan makamai, su ka yi gaba da wadannam mata ba tare da jama’a sun farga ba.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa aka ji Fani-Kayode bai koma APC ba – Yahaya Bello

A cewar wannan mutumi, ‘yan bindigan sun shigo gidan na su ne sadaf-sadaf, su ka kutsa har inda wadannan yara su ke barci, su ka farkar da su.

Bayan ‘yan matan sun farka, sai aka shiga da su cikin jeji, kafin mazan gidan su iya yin wani abu.

Ya ce: “Kun san duka yaran uku su na barci ne a daki guda, da ‘yanuwansu maza su ka ji kara ne, sai su ka bude dakin domin su ga abin da ya faru.”

“Daga nan ne sai ‘yan bindigan su ka fara harbe-harbe a iska, sa’ilin nan sun riga sun tsere da ‘yan matan, su na hanyar shiga cikin daji da su.” inji sa.

KU KARANTA: Za a ba ‘Yan sintiri bindiga domin su yi maganin 'Yan bindiga a Neja

Musiba ta aukawa dangi 1 a Kogi, an sace mata 3 da tsakar dare, an ce sai an biya N100m
Gwamna Yahaya Bello na Kogi Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

‘Yanuwan wannan yara sun samu sun yi magana da wadannan ‘yan bindiga, su ka bukaci a biya Naira miliyan 100 a tashin farko, kafin a fito da yaran.

Yanzu ana kokarin ganin yan bindigan sun rage kudin fansar. Shugaban karamar hukumar Koton Karfe, Isah Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Dazu ne mu ka ji cewa wasu mata rututu sun yi zanga-zanga babu tufafi a jikinsu a gabashin jihar Anambra saboda su nuna wa gwamnati matukar fushinsu.

An yi wannan zanga-zanga ne saboda gwamnatin Jihar Anambra ta na so ta gina filin tashi da saukar jiragen jirgin sama a kauyukan wadannan mata.

Rahotanni sun ce matan nan su na zargin za a nemi a cinye masu filayen noma da su gada ba tare da an yi aikin filin jirgin da gwamna ya ke ikirarin zai yi ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit Nigeria

Online view pixel