CAN za ta sa kafar wando daya da Gwamnatin jihar Kwara a dalilin kawo dokar Hijabi

CAN za ta sa kafar wando daya da Gwamnatin jihar Kwara a dalilin kawo dokar Hijabi

- Kiristocin Najeriya sun yi kaca-kaca da Gwamnan kwara, AbdulRahman AbdulRazaq

- Gwamnatin AbdulRazaq ta hallatawa mata amfani da hijabi a makarantun jihar Kwara

- Kungiyar CAN ta zargi Gwamnan da son-kai da rashin adalci, ta bukaci a janye dokar

Kungiyar CAN ta kiristocin kasar nan ta fito ta yi Allah-wadai da gwamnatin jihar Kwara a dalilin kawo dokar bada iznin amfani da hijabi a makarantu.

Sahara Reporters ta rahoto kungiyar kiristocin Najeriyar ta na zargin gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ta bukaci ya canza wannan matakin.

Sakataren CAN, Joseph Bade Daramola, ya ba Mai girma AbdulRahman AbdulRazaq shawarar ya jira kotu ta zartar da hukunci kafin ya dauki mataki.

Kungiyar ta na zargin cewa an samu wasu da su ke zuwa makarantun da’awar kiristoci a jihar Kwara, su na tursasa wa dalibai mata amfani da hijabi.

KU KARANTA: Ana hana wasu musulmai rajistar katin 'dan kasa saboda hijabi

“Shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya na CAN sun bukaci gwamnan Kwara, Mallam Abdulrahman AbdulRazaq, ya yi maza ya janye matakin da ya dauka na bada iznin amfani da hijabi a makarantun jihar Kwara, har da makarantun kiran kiristoci.”

“Wannan shawara ta zama dole domin mu na ganin gwamnan ya yi gaggawa a kan abin da ke gaban shari’a. Akwai alamin cewa ya na wasa da hankalin kotu, domin gwamnan ya san maganar ta na gaban Alkali, wanda ya yi hukunci a dakata da batun.”

Ya ce: “Mu na kira ga shugabannin siyasa su daina amfani da zafin kishin addini wajen kawo rabuwar kai, su yi adalci ba tare da la’akari da banbancin addini ba.”

KU KARANTA: Wasu sun dura Majalisar Tarayya su na zanga-zanga

CAN za ta sa kafar wando daya da Gwamnatin jihar Kwara a dalilin kawo dokar Hijabi
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Joseph Bade Daramola a madadin CAN, ya ke cewa wannan mataki da aka dauka zai raba kan al’ummar Kwara, kuma ya nuna an fifita wani addini a kan wani.

CAN ta sha alwashin amfani da hanyar da doka ta bada dama domin ayi fatali da wannan umarni.

Kwanakin baya aka ji gwamnan Kwara ya halatta wa ‘dalibai sa hijabi har a makarantun da ake da ta-cewa game da tufafin, sai dai hakan bai yi wa wasu dadi ba.

A karshe har sai da ta kai Gwamnatin Kwara ta garkame wasu makarantu 10 a kan rikicin Hijabin.

Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar ilmi ta Kwara ta fada, da farko an umarci makarantun su bude a makon jiya, amma an fasa yin hakan saboda tsaro.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng