Daruruwan Mata sun fita zanga-zanga da rabin tsiraici saboda Gwamnati za ta gina masu filin jirgi

Daruruwan Mata sun fita zanga-zanga da rabin tsiraici saboda Gwamnati za ta gina masu filin jirgi

- Wasu Matan gabashin Anambra sun fita zanga-zanga a kan filin jirgin da za a gina

- Matan nan sun ce ba za su bada wurinsu a gina filin jirgi, su rasa wurin yin noma ba

- Wadannan mata sun zargi Gwamnatin Anambra da kokarin raba su da filayen na su

A ranar Litinin, 8 ga watan Maris, 2021, wasu mata da-dama a garin Umueri, jihar Anambra su ka yi zanga-zanga da nufin nuna wa gwamnati fushinsu.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wadannan mata sun yi zanga-zangar ne da rabin jikinsu a bude, saboda karfa-karfa da gwamnatin jihar za ta yi masu.

Wadannan mata su na zargin gwamnatin jihar Anambra ta Willie Obiano za ta karbe masu filaye domin ta gina filin tashi da saukar jiragen sama a Umueri.

Matan da su ka yi wannan zanga-zanga da rabin jikinsu a bude sun yi ikirarin cewa gwamna Willie Obiano ya na kokarin karbe filayensu saboda son rai.

KU KARANTA: Idan Allah ya rubuta zan yi mulki a 2023, sai na yi – Yahaya Bello

Rahotanni sun ce a irin wannan yanayi na tsiraici, matan su ka taka har yankin da za a yi filin jirgin saman, su ka hura wuta a kan titi, su na tafe su na ihu.

Matan nan sun sha alwashin ba za a karbe dukiyar da za su bar wa ‘ya ‘yansu da jikokinsu gado ba.

Jaridar ta ce cikin masu wadannan zanga-zanga akwai masu kukan cewa gwamnatin Anambra ta na neman wawurar filayen da su ka fi karfin aikin da za ayi.

Wata ta rubuta: “Obiano ka koma wa 729.606ha na ainihin filin da aka ware domin ayi aikin filin jirgin.”

KU KARANTA: Farashin danyen mai ya na cigaba da tashi a Duniya

Daruruwan Mata sun fita zanga-zanga da rabin tsiraici saboda Gwamnati za ta gina masu filin jirgi
Zanga-zanga a Anambra Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Kauyukan Enuagu, Umuinu da Umuopu sun ba gwamnati fili har 729ha a lokacin da Chris Ngige yake gwamna, amma Obiano ya karbe karin wasu 1200ha.”

Tsoron matan shi ne idan su ka bada filayensu, ba za a samu wurin noma a yankin ba. Duk abin da yake faru wa, gwamnatin Obiano ba ta ce komai ba har yanzu.

Dazu nan ku ka ji cewa Kungiyar CAN ta taso Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a gaba a kan dokar iznin amfani da Hijab da aka kawo a makarantun Kwara.

Gwamnan jihar Kwara ya ce duk wata dalibar da ta ga dama za ta iya zuwa makaranta cikin hijabinta, amma kungiyar CAN ta ce ba za ta yarda da wannan ba.

Kungiyar CAN ta zargi Gwamnan da son-kai da rashin adalci, ta bukaci ya janye wannan dokar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel