Da duminsa: Kotu ta aika tsohon ministan lantarki gidan yari

Da duminsa: Kotu ta aika tsohon ministan lantarki gidan yari

- Alkalin wata babbar kotu da ke Abuja ta bukaci zaman Muhammad Wakil, tsohon ministan lantarki a gidan yari

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da shi a kan zargin almundahanar kudade har N27.1 biliyan

- Kudaden da ake zargin Wakil da yin sama da fadi dasu na tsoffin ma'aikatan hukumar NEPA ne da suka yi murabus

Tsohon karamin ministan wutar lantarki na Najeriya, Muhammad Wakil, zai zauna a gidan yari har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2021 bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ana zargin Wakil da almundahanar kudade har N27 biliyan wanda aka ware domin biyan tsoffin ma'aikatan NEPA hakkinsu na murabus.

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ce ta gurfanar da Wakil a ranar Litinin a kan zarginsa da ake yi da laifuka biyu, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock

Da duminsa: Kotu ta aika tsohon ministan lantarki gidan yari
Da duminsa: Kotu ta aika tsohon ministan lantarki gidan yari. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

An gurfanar da tsohon dan majalisa Wakil tare da wasu kamfanoni biyu, Corozzeria Nigeria Limited da Pikat Properties Nigeria Limited, a kan zarginsu da ake yi da karbar N148 miliyan daga Bestworth Insurance Brokers Limited daga aikin N27.1 biliyan wanda kamfanin inshora ta amince a fitar musu.

KU KARANTA: Da duminsa: Dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Borno

A wani labari na daban, gagararren dan bindiga makiyayi da ke addabar yankin Ibarapaa da Oke- Ogun na jihar Oyo, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma.

Jaridar The Nation ta gano cewa an damke shi a safiyar Lahadi a Igangan dake karamar hukumar Ibarapa ta arewa.

Ana zargin Wakili da zama gagararren dan bindigan da ke jagorantar kashe-kashe da sace mutane a yankunan.

Kehinde Aderemi, mataimaki na musamman a fannin yada labarai ga Aare Ona kakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams Adams ya tabbatar da kamen.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel