Zaƙaƙurin ɗan sandan da aka sace a jihar Edo ya kuɓuta, inji rundunar 'yan sanda

Zaƙaƙurin ɗan sandan da aka sace a jihar Edo ya kuɓuta, inji rundunar 'yan sanda

- Zaƙaƙurin ɗan sandan da aka sace a gidansa a jihar Edo ya samu kuɓuta bayan wani samame da haɗakar ɓangarorin rundunar 'yan sandan jihar suka kai

- Kuɓutaccen ɗan sandan na amsar taimako na musamman a asibiti bayan dawowarsa kamar yadda jami'in yaɗa labaran 'yan sandan jihar ya bayyana

- An sace ASP Clement Amoko da safiyar ranar lahadi a gidansa dake Ogida Quarters na jihar ta Edo

Hankalin rundunar 'yan sandan jihar Edo ya kwanta bayan mataimakin suftitanda na sashen bincike da ƙwaƙƙwafi, ASP Clement Amoko, wanda aka sace da safiyar ran Lahadi ya kuɓuta.

KARANTA ANAN: Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

Zaƙaƙurin ɗan sandan ya kuɓuta ne bayan sashe daban-daban na rundunar 'yan sandan jahar sun shirya wani samame.

Ma'aikacin Jaridar Punch ya gano cewa, Clement Amoko, ya kuɓuta ne a daren ranar ta lahadi.

Bayan haka kuma zaƙakurin ɗan sandan ya samu haɗuwa da iyalansa bayan kuɓuta daga hannun waɗanda suka sace shi.

KARANTA ANAN: Gungun ‘Yan bindiga sun sace mutane 7 a hanya, har da ‘Dan Jariri mai shekara 1 da haihuwa

Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Princewill Osaigbovo, ya tabbatar da faruwar lamarin, saidai yace kuɓutaccen ɗan sandan na amsar kulawa ta musamman a asibiti.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Wanda aka kama ɗin yasha duka a hannun waɗan da suka kamashi.

Wasu mutane ɗauke da bindigu ne suka sace Amoko a gidansa dake, Ogida Quarters a babban birnin jihar ta Edo ranar lahadi.

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gina kowace kilomita ɗaya ta hanyar Abuja-Kano

Hanyar da keda tsawon kilomita 357 zata laƙume 2.23 biliyan akan kowacce kilomita ɗaya.

Da farko dai an fidda ma hanyar 155 biliyan a shekarar data gabata, aka bawa kamfanin 'Julius Berger' amma aikin yaƙi gamuwa.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: