Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA, ya aika sako ga masu safarar miyagun kwayoyi

Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA, ya aika sako ga masu safarar miyagun kwayoyi

- A karshen makon jiya ne sanarwa ta fito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

- An kirkiri hukumar NDLEA ne domin yaki da sha da kuma fatauci da safarar miyagun kwayoyi a Nigeria

- A ranar Litinin ne Buba Marwa ya shiga Ofis tare da aika muhimmin sako ga masu harka da miyagun kwayoyi

Sabon shugaban hukumar NDLEA mai yaki da miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya shiga Ofis bayan sanar da nadinsa a karshen makon jiya.

Marwa ya fara da aika sakon gargadi ga masu sha, safara, da duk wata mu'amala da miyagun kwayoyi akan su dakata haka ko kuma su fuskanci fushin NDLEA, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Da ya ke gabatar da jawabi a gaban taron manyan jami'an hukumar da suka halarci wurin, Marwa ya bayyana cewa; "alhakin hukumar NDLEA ne ta dakatar da wannan shirmen tu'ammali da miyagun kwayoyi a Nigeria".

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

"A matsayinku na masu yaki da abin, kun san irin illolin da amfani da miyagun kwayoyi suka yi wa kasa. Babu wani lungu ko wata al'umma a Nigeria da matsalar amfani da miyagun kwayoyi ba ta addaba ba."

Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA, ya aika sako ga masu safarar miyagun kwayoyi
Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA, ya aika sako ga masu safarar miyagun kwayoyi
Asali: Twitter

Marwa ya bayyana dole sai an kawo sauye-sauye da kara karfin hukumar NDLEA domin ta samu dama da sukunin yin aiki kamar yadda ya kamata.

KARANTA: An samu kwayar cutar korona a 'Ice Cream'

Kazalika, ya bayyana cewa nan bada dadewa zai fito da wani daftarin tsarin aiki a hukumar NDLEA wanda za'a kaddamar a tsakanin 2021 zuwa 2025.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa rahoton yadda ake fusakantar karuwar yara matasa da ke zukar sinadarin 'Sholisho' a jihar Kano.

Jihar Kano ta yi kaurin suna wajen matsalar yawaitar matasa da ke amfani da kayan maye daban-daban.

A cikin shekarar 2019, hukumomi sun bayyana Kano a matsayin jiha ta uku da ake da yawan masu shaye-shaye a Nigeria da adadin fiye da kaso 70% na matasa da ke amfani da kayan maye.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: