An yi wa mutune fiye da miliyan 2 rajistar APC a jihar Kano, in ji Ganduje

An yi wa mutune fiye da miliyan 2 rajistar APC a jihar Kano, in ji Ganduje

- Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce a ƙalla mutane 2.5 miliyan aka yi wa rajistan APC a Kano

- Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC da aka yi a Kano

- Ganduje ya ce akwai yiwuwar za a yi wa mutum miliyan uku zuwa huɗu rajistar kafin a kammala aikin sabunta rajistar da yin sabbi

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam'iyyar APC, kawo yanzu, ta yi wa mambobi miliyan 2.5 rajista a aikin rajistar/sabunta rajista a jihar Kano.

Sakataren watsa labarai na gwamnan, Abba Anwar ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Kano, rahoton Premium Times.

DUBA WANNAN: Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

An yi wa mutum miliyan 2.5 rajistar APC a jihar Kano, in ji Ganduje
An yi wa mutum miliyan 2.5 rajistar APC a jihar Kano, in ji Ganduje. Hoto: @PremiumTimesNg
Asali: Facebook

Mr Anwar ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC karo na shida da aka yi a Kano.

"Dukkan mu mun san cewa an ƙarar da takardun rajista 100 na farko. An kuma ƙarar da 200 na biyu.

"Idan aka cigaba da haka ana iya yi wa mambobi miliyan uku ko huɗu rajista a jihar," in ji shi.

KU KARANTA: Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi

Gwamnan ya kuma bukaci wadanda ke rajistar su tabbatar sun yi adalci.

"Kada a nuna wariya. Duk wanda ke son rajistar shiga gagarumar jam'iyyar mu a yi masa kuma hakan na cikin hikimar da yasa jam'iyyar mu ke cigaba," in ji shi.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da sarautu na jihar, Murtala Gari ya ce takardun rajistar da hedkwatar jam'iyyar na ƙasa ta bawa jihar Kano ba su wadata ba don haka suna buƙatar ƙari.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel