‘Yan bindiga sun dura Sokoto, sun hallaka matasa da ‘yan sa-kai 15 a tsakar dare

‘Yan bindiga sun dura Sokoto, sun hallaka matasa da ‘yan sa-kai 15 a tsakar dare

- ‘Yan bindiga sun sake kai hari a karamar hukumar Sabon-Birni a jihar Sokoto

- An hallaka wasu matasa, ‘yan sa-kai da wata ‘yar shekara 6 cikin duhun dare

- A ‘yan kwanakin an kai hare-hare a jihohin Zamfara, Neja, Kaduna da Katsina

‘Yan bindiga sun shiga wani kauye da ake kira Tanau, a karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, inda su ka hallaka Bayin Allah rututu a yau.

Jaridar Sahelian Times ta rahoto cewa wannan mummunan lamarin ya auku ne da kimanin karfe 1:00 na dare a ranar Juma’a, 5 ga watan Maris, 2021.

Wani wanda abin ya auku a gaban idanunsa, ya fada wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun rika harba bindigogi ta ko ina da su ka shigo kauyen.

Majiyar ta kara da cewa: “Hakan ya sa dole mutane su ka rika gudu domin su tsira da rayuwarsu.”

KU KARANTA: Ba zan yi sulhu da 'yan bindiga ba - Gwamna Bello

Yake cewa “Lokacin da su ka iso, sai su ka fara harba harsashi ta ko ina, su ka rika bi gida zuwa gida su na neman dabbobi da kuma wasu kaya masu daraja.”

“Bayan sun gama kai hari, sai su ka tsere, sun tafi da kayan da duk su ka sace, amma sai wasu matasan kauyen da ‘yan sa-kai su ka bi su zuwa cikin jeji.”

“Abin takaici, da matasan su ka isa dajin, sai su ka kai masu samame, su ka kashe da yawa daga cikinsu.”

Kamar wannan mutumi ya bayyana, za a birne wadanda aka kashe a yau yadda addinin musulunci ya tanada, ragowar da su ka yi rai, su na jinya a asibiti.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun kama maras gani da yake damfarar mutane

‘Yan bindiga sun dura Sokoto, sun hallaka matasa da ‘yan sa-kai 15 a tsakar dare
Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Hoto: thisdaylive.com
Source: UGC

A wani kaulin, ‘yan bindigan sun yi sa’a biyu su na harbe-harbe, su ka kashe har da wata karamar yarinya mai shekara 6 a Tara, a kauyen Hillu da ke Sabon-Birni.

Gwamna Nyesom Wike ya bada labarin yadda ya yi addu'a ka da a samu tsaro a kasar nan saboda abinda shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa jihar Ribas a 2016.

A jawabin da Nyesom Wike ya yi wurin bude asibitin gidan gwamnati, ya ce ya nemi taimako daga wurin gwamnatin shugaba Buhari ne amma aka hana shi.

Gwamnan ya yi addu'a Allah ya wanzar da rashin tsaro har sai Shugaban kasa ya nemi afuwar Ribas.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel