Dahiru Bauchi: Ba na iya tuna abubuwa, amma ba zan manta da abin da El-Rufai ya yi mani ba

Dahiru Bauchi: Ba na iya tuna abubuwa, amma ba zan manta da abin da El-Rufai ya yi mani ba

- Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fadi abin da ba zai taba barin zuciyarsa ba

- Babban malamin musuluncin ya soki kokarin hana bara da gwamnoni ke yi

- Shehin ya ce duk shugaban da ya ke taba Al-kur’ani zai rabu da Musulunci

BBC Hausa ta yi hira da babban malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin shirinta na ‘daga bakin mai ita.’

An yi wa fitaccen malamin darikar tijjaniyar tambayoyi da-dama, inda shi kuma ya bada amsoshi.

Daga cikin tambayoyin da aka yi wa Dahiru Usman Bauchi mai shekara 93 a Duniya shi ne abin da aka yi masa da ba zai taba manta wa ba.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ganin tsufa ta kama shi (kusan shekara 100), ya manta mafi yawan abubuwan da suka faru da shi a rayuwa.

KU KARANTA: Jami'ai sun shiga gidan Dahiru Bauchi, sun yi gaba da Almajirai

A cewar shehin, abin da ya auku kwanan nan da ba zai manta ba shi ne yadda gwamna ya bada umarni aka shigo gidansa aka dauke masa almajirai.

Dahiru Usman Bauchi ya ce an zo da motoci da bindigogi, aka tattara yaran da su ke koyon karatun Al-Qur’ani a gidansa, da sunan haramta bara.

Ko da cewa Malamin bai kama suna ba, amma gwamnatin Nasir El-Rufai ce ta yi wannan aiki.

Dahiru Bauchi ya yi wa gwamnonin kashedin cewa Ubangiji zai yi azaba ga duk wanda ya yi yunkurin yin fito-na-fito da masu karatun Al-kur’ani.

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni su daina tsangwamar almajirai

Dahiru Bauchi: Ba na iya tuna abubuwa, amma ba zan taba mantawa da abin da El-Rufai ya yi mani ba
Dahiru Bauchi tare da Shugaban kasa Hoto: BBC
Asali: UGC

Babban malamin ya ce kamar yadda Allah bai kyale mutanen Annabi Salihu ba, duk wanda ya taba Al-Kur’ani, ba zai gama da Duniya lafiya ba.

A game da sarakunan gargajiya, Shehin ya ce ya fi samun alaka mai kyau da fadar Kano musamman a lokacin Sarki Muhammadu Sanusi I.

A wannan hirar da aka yi da Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Kur'ani, kamar yadda aka san shi da baiwar hadda.

Dahiru Bauchi yace iyayensa da kakanninsa ne suka fara samo masu sirri da lakanin haddar Al-kur'ani daga wajen kabilar Bare-bari a kasar Borno.

Shehin yake cewa bayan zuwan Sheikh Ibrahim Inyass, ya roka wa mutane saukin yin hadda.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel