Rayyuka 13 sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a Sokoto

Rayyuka 13 sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a Sokoto

- Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Tara a jihar Sokoto sun halaka mutum 13

- Ƴan bindiga sun kuma raunata mutane bakwai sannan sun sace kayan abinci

- Dagacin garin Tara, Mainasara Mohammed Tara ya tabbatar da afkuwar harin

Ƴan bindiga sun halaka mutane 13 a kauyen Tara da ke karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun kuma raunata wasu mutum bakwai a halin yanzu suna asibiti suna jinya.

Rayyuka 13 sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a Sokoto
Rayyuka 13 sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a Sokoto. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar dagacin garin Tara, Mainasara Mohammed Tara, ƴan bindigan sun sace dabbobi masu yawa bayan sun ƙona musu rumbun ajiyar kayan abinci.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

"Misalin ƙarfe 11.58 na dare suka zo ta wata hanya da ba a saba bi ba domin matasan mu da maza na gadin manyan hanyoyin.

"Ba mu barci cikin dare saboda yawan hare-haren da suke kawo mana.

"Mun raba kanmu ta yadda kowacce tawaga za ta riƙa gadin kofar shigowa garin.

"Don haka sai suka sulolo suka shiga garin to gabashin suka bude wa mutanen mu wuta suka kashe su.

"Daga nan suka ƙarasa cikin gari suna kashe duk wanda suka hadu da shi.

"Mun birne mutum 13 ciki har da yarinya mau shekaru shida sannan mutum bakwai sun jikkata suna asibiti suna jinya," a cewar Mohammed.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama

Ya ce ƴan sa kai da suka tuntuba tunda farko ba su amsa kirar su ba.

Muhammad ya ce wanna shine karo na biyu da ake kai musu hari cikin watanni biyu inda ya ce ya rasa dabbobi 200 a harin na baya.

Da aka tuntube shi, kakakin ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar ya ce zai bada cikakken bayani idan ya dawo daga ƙauyen.

"Yanzu haka muna hanyar zuwa ƙauyen don ganin abinda ya faru. Zan muku bayani idan na dawo," in ji shi.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel