Lokacin zanga-zangar #EndSARS, an shiga fada an sace mani $2m, N17m inji Sarkin Legas

Lokacin zanga-zangar #EndSARS, an shiga fada an sace mani $2m, N17m inji Sarkin Legas

- Oba Rilwan Akiolu ya yi magana a kan abin da ya faru lokacin #EndSARS

- Sarkin na Legas yace abin da aka sace daga fadarsa ya kai Naira miliyan 800

- Mai martaba Rilwan Akiolu ya nemi gwamnatin tarayya ta ba Legas agaji

Oba na kasar Legas, Mai martaba Rilwan Akiolu, ya ce an wawuri kudi fam Dala miliyan $2 da kuma wasu Naira miliyan 17 daga fadarsa a shekarar bara.

Mai martaba Rilwan Akiolu ya ce matasan da su ka kawo hari a fadarsa a lokacin da ake zanga-zangar #EndSARS ne su ka yi awon-gaba da wadannan kudi.

Kamar yadda Sarkin ya bayyana, an yi masa wannan sata ne a ranar 21 ga watan Oktoba, 2020. Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba da yamma.

A lokacin da ake wannan zanga-zanga ta #EndSARS, wanda ta yi kamari a Legas, an auka har fadar Oba da ke yankin Iga Idugaran a unguwar Lagos Island.

KU KARANTA: Sarkin Ondo ya rasu bayan shafe shekaru 43 kan karagar mulki

Wadannan fusatattun matasa sun yi barna a fadar, su ka lalata motoci, su ka saci kaya, har su ka tsere da wata sandar girma ta mai martaba da ake kira Opa Ase.

Da take magana wajen kaddamar da wani sabon gini a jiya, Oba Rilwan Akiolu ya ce ya daina fadar irin asarar da ya yi idan ya na magana a bainar jama’a.

Sarkin yake cewa ya yi asara ba ta wasa ba a lokacin da ake yi wa ‘yan sanda zanga-zanga, ya ce wadanda su ka kai masa hari, ba su fahimci barnar da su ka yi ba.

“An kona gine-gne da dama, da motocin da su ke kawo kudi. Yanzu zan iya fitowa gaban Duniya in bayyana cewa an sace $2m da N17m daga fada ta.” Inji Oba.

Lokacin zanga-zangar #EndSARS, an shiga fada an sace mani $2m, N17m inji Sarkin Legas
Mai martaba Oba Rilwan Akiolu
Source: Twitter

KU KARANTA: Babur ya kashe daya daga cikin ‘Ya ‘yan Dahiru Mangal a Katsina

Oba Akiolu ya ce babu inda aka yi asara a lokacin kamar Legas, don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wa jihar da tallafi domin a rage asarar da aka yi.

Idan za ku tuna Oba Rilwan Akiolu ya kai ziyarar kara ga tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a gidansa da ke Legas, a lokacin da aka cire masa rawani.

A daren Lahadi, 15 ga watan Maris ne Malam Muhammadu Sanusi II ya isa jihar Legas bayan kotu ta bada umarnin sakinsa daga tsarewar da aka yi masa a Nasarawa.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Abdullahi Ganduje ta Kano ta sauke shi daga gadon sarauta.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel