Yanzu-yanzu: Hatsari ya ritsa da ayarin motocin gwamnan Gombe

Yanzu-yanzu: Hatsari ya ritsa da ayarin motocin gwamnan Gombe

- Ayarin motoccin gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, sun yi hatsari a hanyarsu ta komawa Gombe daga Bauchi

- Mutum daya, direban mota bas ya riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin da ya faru a hanyarsu na komawa Gombe bayan hallartar taron gwamnonin Arewa maso gabas

- Shugaban hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, reshen jihar Bauchi,Yusuf Abdullahim ya tabbatar da afkuwar hatsarin

'Yan jarida da dama cikin ayarin motocin gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, a ranar Alhamis sun yi hatsari a hanyarsu ta komawa Gombe daga Bauchi. Direban motar ya rasu.

Gwamnan na Gombe ya tafi Bauchi ne a ranar Laraba domin hallartar taron gwamnonin jihohin Arewa masa Gabas karo na hudu da aka yi a jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Yanzu-yanzu: Hatsari ya ritsa da ayarin motocin gwamnan Gombe
Yanzu-yanzu: Hatsari ya ritsa da ayarin motocin gwamnan Gombe. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnan ya tsaya har zuwa ranar Alhamis domin halartar bikin daura tubalin gini da gyaran gidan gwamnatin jihar Bauchi da shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa maso Gabas, Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi.

A halin yanzu babu cikakken bayani game da hatsarin amma wakilin The Punch ya gano cewa hatsarin ya faru ne kusa da iyakar Gombe da Bauchi.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Borno, Adamawa, Gombe da Bauchi, yayin da mataimakan gwamnonin Yobe da Taraba suka wakilce su.

A halin yanzu babu cikakken bayani game da hatsarin amma wakilin The Punch ya gano cewa hatsarin ya faru ne kusa da iyakar Gombe da Bauchi.

KU KARANTA: Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

Direktan watsa labarai na jihar Gombe, Samail Uba Misilli shima yana cikin motar tare da wasu yan jarida da suka yi wa gwamnan rakiya zuwa Bauchi don hallartar taron.

A halin yanzu ba a tabbatar idan mutanen cikin motar sun samu rauni ba amma majiyar Legit.ng ta gano cewa motar ta yi kundunbala sau uku.

Shugaban hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, reshen jihar Bauchi,Yusuf Abdullahim ya tabbatar da afkuwar hatsarin amma bai iya bada cikaken bayani ba domin a yankin Gombe abin ya faru.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel