Gwamnati ta haramta hake-haken ma’adai a Jihar Zamfara

Gwamnati ta haramta hake-haken ma’adai a Jihar Zamfara

– Gwamnatin Tarayya ta hana hako arzikin kasa a cikin Zamfara

– Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya bayyana mana wannan

– IG Mohammed Adamu ya nemi Baki su fice daga cikin Yankunan

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hana cigaba da duk wani aiki na hako ma’adanai a kasar jihar Zamfara. Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya watau Mohammed Adamu shi ne ya bayyana wannan ba da dadewa ba.

A Ranar Lahadin nan, 7 ga Watan Afrilun 2019, gwamnatin kasar nan ta bada sanarwar cewa an dakatar da duk wani aiki da ya shafe hake-haken kayan arzikin kasa a Zamfara, a dalilin rikicin da ake ta fama da shi a jihar.

Shugaban ‘yan sandan kasar, IGP Mohammed Adamu ya bayyana wannan matsaya na gwamnatin Najeriya ne a babban birnin tarayya Abuja dazu lokacin da yake ganawa da manema labarai da ke cikin fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Malamin addini ya fadawa Buhari abin yi a kan rikicin Zamfara

Mohammed Adamu yace gwamnati ta gano cewa akwai alaka tsakanin masu tada kafar baya a jihar Zamfara da kuma wadanda ke hako ma’adanai a boye. Wannan ya sa aka hana kowa cigaba da hake-hake a fadin jihar.

Bayan nan kuma gwamnatin Najeriyar tayi umarni ga duk mutanen kasar waje da ke hakon kayan arzikin kasa da su tattara su bar wadannan yankuna da ke dauke da alatu na arzikin gwal da kuma sinadarin karfe na kirar lid.

Wadanda ke nan a lokacin da aka dauki wannan mataki sun hada da babban Hadimin shugaban kasa watau Malam Abba Kyari da kuma Darektan hukumar DSS, Yusuf Bichi da shugaban hukumar NIA na kasa watau Ahmed Rufai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel