Karin bayani: Abin da matakin da Buhari ya dauka na haramtawa jirgi shawagi a Zamfara yake nufi

Karin bayani: Abin da matakin da Buhari ya dauka na haramtawa jirgi shawagi a Zamfara yake nufi

- Gwamnatin Tarayya ta hana duka wasu jiragen sama tashi a jihar Zamfara

- Ba a taba samun lokacin da gwamnati ta haramta tashin jirgi a wata jiha ba

- Gwamnati ta ce hakan zai yi maganin matsalar tsaron da jihar ke fuskanta

A karon farko a tarihin kasar nan, gwamnatin tarayya ta haramta tashin jirgi a jihar Najeriya saboda mummunar matsalar rashin tsaro.

Jaridar The Cable ta yi karin haske game da abin da wannan mataki da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka yake nufi.

A mulkin farar hula ba a taba ganin irin wannan ba, sai dai illa iyaka, a 2017, gwamnatin tarayya ta hana tashi a filin jirgin Abuja saboda gyara.

Kasashen da su ka dauki irin wannan mataki a shekarun bayan nan su ne: Libya da Armenia.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun karbi N5m, sannan sun harbe Attajiri

Kamar yadda Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Babagana Monguno ya bayyana yadda wannan zai yi maganin ‘yan bindiga.

Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce: "Makasudin daukar wannan mataki shi ne gwamnati ta karbe wuraren da su ka fada hannun miyagu."

Daga yanzu babu wani jirgin sama da zai tashi a sararin samaniyar jihar Zamfara, hakan kuwa ya na nufin ko da babu matuki a cikin jirgin saman.

Dalilin hakan shi ne zai sa jami’an tsaro su samu iko da yankin. A Zamfara ana fama da rashin tsaro.

KU KARANTA: Kasuwar ‘yan bindiga ta na ci, an yi cinikin kudin fansar N10bn a 2021

Karin bayani: Abin da matakin da Buhari ya dauka na haramtawa jirgi shawagi a Zamfara yake nufi
Shugaban kasa Buhari da Gwamna Matawalle Hoto: www.vanguardngr.com
Source: UGC

Masana sun ce mafi yawan lokaci idan aka dauki wannan mataki, ‘yan ta’adda su kan huce ne a kan gama-gari, su rika kai masu hari ta kasa.

Tsoron da ake yi shi ne ‘yan bindiga na amfani da mutanen da su ka yi garkuwa da su a matsayin kariya, su hana ayi masu luguden wuta daga sama.

A yau ne mu ke ji cewa wata kungiyar Ibo ta buƙaci a cafke Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi saboda maganganu da ya ke yi ya na kare ƴan bindiga.

Kungiyar ta fusata ne bayan Gumi ya kwatanta ƴan bindiga da tsohon jagorar Ibo marigayi Chukwuemeka Ojukwu, wanda ya jagoranci Biyafara.

The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC, ta yi kira ga hukumomin tsaro su yi ram da Malamin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel