Yaron Shugaban Kasa ba ya cikin hayyacin sa tun bayan hadarin babur

Yaron Shugaban Kasa ba ya cikin hayyacin sa tun bayan hadarin babur

- Kwanan na ‘Dan Shugaba Buhari ya gamu da hadarin babur

- Fadar Shugaban Kasa dai ta ce saurayin ya fara samun sauki

- Amma mun ji cewa Yusuf Buhari bai san inda yake ba a yanzu

Idan ba ku manta ba kun ji labari cewa Yusuf Buhari yayi hadari a Ranar Talatar nan da ta wuce a Babban Birnin Tarayya Abuja sa’ilin da yake kan wani babban babur na zamani inda yanzu yake asibiti.

Yaron Shugaban Kasa ba ya cikin hayyacin sa tun bayan hadarin babur
Yaron Shugaban Kasa Yusuf Buhari kwanakin baya

Fadar Shugaban Kasa tace ya samu sauki amma wasu rahotanni sun musanya hakan. Labari na zuwa mana cewa ana kokarin shekawa da yaron Shugaban Kasa Muhammadu Buhari watau Yusuf zuwa wani asibiti a Kasar Jamus domin ganin manyan Likitoci.

KU KARANTA: Karin bayani game da hadarin ‘Dan Shugaban Kasa Yusuf Buhari

Mun ji cewa Yusuf Buhari bai san inda yake ba a halin yanzu da mu ke magana. Yaron Shugaban Kasar ba ya cikin hayyacin sa tun bayan hadarin babur din da yayi kuma yanzu haka yana bangaren ICU na rai-hannun Allah a sashen asibitin da ake duba sa.

Rahotanni daga Jaridar The Cable sun nuna cewa har wasu Likitoci na tsoron duba sa gudun wani abu ya faru su shiga cikin wani hali don kuwa shi kadai ne Yaron Shugaban Kasar a Duniya. Ana dai tunani a samu jirgi a wuce da shi asibitin Jamus a Turai.

Majiyar tace Yusuf ya samu hadarin ne bayan da yayi kokarin tserewa wani abokin sa a kan babur daga nan ne yayi kuli-kulin-kubura a kna titi. Mahaifiyar sa Hajiya Aisha Buhari dai ta nemi a garzaya da shi asibiti inda ya samu rauni a kai da kuma wasu karaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel