Tubabbun ƴan ta'adda na komawa Boko Haram bayan leƙen asirin jama'a, in ji Zulum

Tubabbun ƴan ta'adda na komawa Boko Haram bayan leƙen asirin jama'a, in ji Zulum

- Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce shirin sauyawa yan Boko Haram tunani na Safe Corridor baya cimma manufar da aka yi don ita

- Zulum ya ce sau da yawa tubabbun yan ta'addan da suka amfana da shirin sukan koma su shiga kungiyar Boko Haram bayan sun tattara bayannan sirri kan jama'an unguwanninsu

- Don haka Zulum ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da a yi wa tsarin garambawul tare da gaggauta shari'a da hukunta yan ta'adda

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce tsarin sauya tunanin yan ta'addan Boko Haram da ake kira 'Safe Corridor' baya aiki kamar yadda aka yi tsamanni.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a wurin taron kungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas da aka yi a ranar Laraba a Banquet Hall, gidan gwamnati da ke Bauchi, rahoton The Punch.

Tubabbun ƴan ta'adda na komawa Boko Haram bayan leken asirin jama'a, in ji Zulum
Tubabbun ƴan ta'adda na komawa Boko Haram bayan leken asirin jama'a, in ji Zulum. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

Wadanda suka hallarci taron sun hada da gwamnonin jihohin orno, Adamawa, Gombe da Bauchi, yayin da mataimakan gwamnonin Yobe da Taraba suka wakilce su.

A cewar Zulum, wadanda suka amfana da shirin na sauya tunani da koyar da sana'a sukan koma su shiga kungiyar ta'addan bayan sun tattara bayannan sirri kan jama'an unguwanninsu da dama ba su fiye son zama tare da su ba.

Don haka Zulum ya ce akwai bukatar a sake duba tsarin a yi bita ko garambawul.

"An tabbatar cewa tsarin sauya tunanin 'yan ta'adda ko Safe Corridor baya aiki kamar yadda aka yi tsammani. Mafi yawancin lokuta, wadanda aka sauya wa tunanin suan koma su shiga kungiyar ta'addancin bayan sun kwashe lokaci suna nazarin yanayin tsaro a garuruwansu.

"Har wa yau, mutanen gari su kansu ba su cika son tubabbun yan ta'addan na zama cikinsu ba saboda munanan ayyukan da suka yi a baya," wani sashi cikin jawabin Zulum.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

Gwamnan na Borno ya ce abinda ya fi dacewa shine a yi wa yan ta'addan shari'a bisa tanadin dokar Ta'addanci ba tare da bata lokaci ba, sai dai wadanda aka gano tilas yasa suka shiga da aka ceto ko suka tsere sune za a iya duba yiwuwar sauya wa tunani.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel