‘Yan bindiga sun addabi Kaduna, sun kashe mutane 6 a hari na 4 a cikin kwana 2

‘Yan bindiga sun addabi Kaduna, sun kashe mutane 6 a hari na 4 a cikin kwana 2

- An hallaka mutane shida a wasu hare-hare da aka kai a jihar Kaduna

- Gwamnatin Kaduna ta ce an bar wani mutum daya ya na jinya a asibiti

- ‘Yan bindiga sun aukawa wasu kauyuka a garuruwan Igabi da Kauru

Mutane shida aka rahoto cewa sun mutu a wasu danyen hare-hare da ‘yan bindiga su ka kai a kananan hukumomin Kauru da Igabi, jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun kai hari ranar Talata a garin Birnin Yero, a karamar hukumar Igabi.

Kamar yadda kwamishinan na Kaduna ya bayyana, ‘yan bindigan sun tare hanya, su ka hallaka wani Bawan Allah da ake kira Hussaini Suleiman Dari.

Haka zalika, miyagun sun raunata wani Malam Dahiru Saidu, yanzu ya na jinya a gadon asibiti. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto dazu da rana.

KU KARANTA: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun fatattaki 'Yan Boko Haram

A kauyen Gwada da ke karamar hukumar ta Igabi, miyagun sun kai hari, su ka kashe wasu mutane biyu; Yahuza Sale da Garba Sule.

A wani kauye da ake kira Amawan Dadi Rugan Jauru a Kauru, an kashe wani mutum guda. Rahotanni sun ce ana kiran wannan Bawan Allah da ‘Likita’.

Jaridar ta ce gwamnatin Kaduna ta aika ta’aziyyarta ga iyalin wadanda su ka riga mu gidan gaskiya.

Samuel Aruwan yake cewa Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya aika sakon ta’aziyyarsa ga mutanen da wannan ta’adi ya shafa.

KU KARANTA: Boko Haram sun sace ma'aikata 7 a Borno

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi wa iyalin wadanda su ka yi wannan rashi addu’ar Ubangiji ya yi masu rahama, sannan ya yi wa wanda ke jinya addu’ar samun sauki.

Dazu kun ji cewa wasu yan bindigan sun kar farmaki jihar Kaduna inda suka halaka mutane kimanin su goma a cikin 'yan kwanakin da su ka gabata.

Rahotanni sun ce an banka wa gidaje 10 da babura biyu da buhuhunan citta guda 50 wutaa garin Zangon Kataf da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Ana zargin Fulani da ke yankin Kakwa a kasar Atyap a Zangon ne su ka kai wannan harin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel