Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Jangebe, garin aka sace dalibai, an kashe mutum 1

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Jangebe, garin aka sace dalibai, an kashe mutum 1

Akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa yayinda da dama sun jikkata a Jangebe, garin da aka sace dalibai mata a jihar Zamfara makon da ya gabata.

Bayan da daliban suka kubuta daga hannun yan bindiga, gwamnati ta kaisu asibiti domin duba lafiyarsu da kuma tattaunawa da su.

A ranar Laraba, an mayar da su makarantar domin sadasu da iyayensu.

Amma, wasu matasa a garin suka fara kaiwa duk wanda ya karaso hari.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin garin ya ce jami'an tsaro sun kashe mutum daya yayinda suke kokarin kwantar da kuran.

Saurari karin bayani...

Asali: Legit.ng

Online view pixel