‘Yan Sanda da Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rubdugu, sun hallaka tsageru a kauyukan Katsina

‘Yan Sanda da Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rubdugu, sun hallaka tsageru a kauyukan Katsina

- Jami’an tsaro sun kashe ‘Yan bindiga rututu a wasu garuruwan jihar Katsina

- ‘Yan Sanda da Sojoji sun kai farmakin hadin-gwiwa, sun kashe wasu Miyagu

- An kashe ‘Yan bindiga ne a Safana, an lallasa Miyagu a Kankara da Dandume

Akalla ‘yan bindiga takwas ne sojoji su ka hallaka yayin da su ka kai wani harin hadin-gwiwa a karamar hukumar Safana, jihar Katsina, inji jaridar Punch

A ranar Lahadi, 28 ga watan Fubrairu, 2021, sojoji da ‘yan sanda su ka kammala sinitirin da su ka yi, inda su ka auka wa ‘yan bindigan da su ka fake a Safana.

Jami’an tsaron sun yi nasarar karbe bindiga kirar AK-47, sannan sun kona babura tara na ‘yan bindigan.

Mai magana da yawun bakin dakarun ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar mana da wannan da ya yi hira da manema labarai a ranar Litinin.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya aikawa Buhari wasika kan rashin tsaro

Gambo Isah yake cewa dakarun sun kai harin ne a yankin kauyukan Guzurawa da Garin Gambo.

Da yake jawabi, a madadin ‘yan sanda ya ce: "An hallaka ‘yan bindiga 8, an gano wasu babura 9 da aka kona, an samu bindigar AK-47 da casbi biyar na harsashi."

“Ana cigaba da kai farmaki domin yakar matsalar ta’adin ‘yan bindiga, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuffuka.” Inji Gambo Isah.

Haka zalika, jami’an tsaron sun yi ram da wasu ‘yan bindiga a kauyen Zango, karamar hukumar Kankara, har su ka samu bindigar AK-47 da wasu harsashai.

KU KARANTA: Lauyoyi sun rubutawa DSS takarda a kan tsare tsohon Hadimin Ganduje

‘Yan Sanda da Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rubdugu, sun hallaka tsageru a kauyukan Katsina
Shugaban 'Yan Sanda na kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Twitter

A makon da ya gabata, ‘yan sandan Katsina sun cafke wani Usman Ahmed, a titin Sabon Barka, karamar hukumar Dandume, Katsina, mai garkuwa da mutane.

A ranar Lahadi ne masu garkuwa da mutane su ka barko da tsakar dare su ka sace ‘Dan kasuwa a garin Illela. Sunan wannan mutum, Alhaji Rabi’u Amarawa.

‘Yan bindiga sun buda wa Jami’an sa-kai wuta yayin da su ka je ceto wannan Attajirin mutum.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng