Mutane 12 sun mutu wajen ceto Mai kudin da 'Yan bindiga su ka yi garkuwa da shi a Sokoto
- ‘Yan bindiga sun sace wani shahararren ‘Dan kasuwa da ke garin Illela
- Wasu sun nemi su ceto Alhaji Rabi’u Amarawa daga hannun Miyagu
- A sanadiyyar haka ‘Yan sa-kai 12 su ka rasa ransu a Illela Amarawa
Mutane 12 aka rahoto cewa sun rasa ransu a yayin da ake kokarin ceto wani Bawan Allah da aka yi garkuwa da shi a garin Illela Amarawa, a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan bindiga sun shigo karamar hukumar Illela da tsakar dare a ranar Litinin, su ka yi gaba da wani Alhaji Rabi’u Amarawa.
Wannan mutumi da aka yi awon gaba mashahurin ‘dan kasuwa ne da ake ji da shi a Illela Amarawa.
Iyalan wannan mutum sun yi maza sun sanar da jami’an tsaron sa-kai game da abin da ya faru, inda su kuma su ka tada wata runduna domin su je, su ceto shi.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Tsohon Sanatan Kaduna da Gwamnan Neja sun yi cacar-baki
A lokacin da su ka je kubuto ‘dan kasuwar, sai ‘yan bindigan su ka buda masu wuta. A nan take mutane 12 su ka mutu, daga ciki har da kanin Rabi’u Amarawa.
Wani mazaunin Illela Amarawa, ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa an kashe wadanda su ka je kubuto Alhaji Amarawa, ya ce: “Yanzu nan mu ka gama birne mutane 10.”
Ya ce: “Sun zo gidanshi ne kai-tsaye, su ka yi gaba da shi, kamar shi kadai kawai su ke nema. Gidansa bai wuce kilomita guda daga asalin cikin birnin Illela ba.”
Wannan mutum da yake kamar ‘da wajen Rabi’u Amarawa, ya ce a halin yanzu su na cikin makoki.
KU KARANTA: Lauyoyi sun rubutawa DSS takarda a kan tsare tsohon Hadimin Ganduje
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce an rasa rayuka sosai.
ASP Sanusi Abubakar ya ce jami’an sa-kan ba su tuntubi ‘yan sanda ba, sai kawai su ka tashi, su ka dumfari wadannan miyagun ‘yan bindiga cikin tsakar daren.
Yanzu nan mu ke ji daga HumAngle cewa Yara 317 da aka sace daga makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara sun dawo gida.
An rahoto Majiyar ta na cewa: “Alhamdulillah! Ina matukar farin ciki da sanar da sakin daliban makarantar GGSS Jangebe da masu garkuwa da mutane su ka sace.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng