Dawo-dawo: Magoya-baya sun fara yi wa Jonathan yakin neman zaben Shugaban kasa

Dawo-dawo: Magoya-baya sun fara yi wa Jonathan yakin neman zaben Shugaban kasa

- Magoya baya sun kaddamar da tafiyar ‘Goodluck Must Run 2023 Movement’

- Ana kokarin jawo hankalin Goodluck Jonathan ya sake neman takara a 2023

- Masoyan tsohon shugaban su na so gwaninsu ya karasa ragowar wa’adinsa

Yayin da wasu su ke kiran tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake neman takara, wasu har sun kai ga fara nema masa goyon baya a Bayelsa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kaddamar da tafiyar ‘Goodluck Must Run 2023 Movement’ da nufin tsohon shugaban Najeriyar ya sake hawa mulki.

Wadannan magoya baya su na kokarin ganin Dr. Goodluck Jonathan ya yi takara domin ya kara yin mulkin kasar nan kamar yadda ya yi tsakanin 2010-2015.

Jagororin wannan tafiya ta ‘Goodluck Must Run 2023 Movement’ sun fara tuntubar masu ruwa da tsaki da nufin a ja hankalin Jonathan ya shiga takarar 2023.

KU KARANTA: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takarar Jonathan a APC

Shugaban wannan tafiya, Fasto London Brown da sakatarensa, Jones Ebi, sun fitar da jawabi a ranar Litinin, su ka fadi abin da ya sa su ke tare da Jonathan.

London Brown da Jones Ebi sun bayyana cewa su na so tsohon shugaban ya dawo mulki ne domin arziki ya shiga hannun kowane bangare na ‘Yan Najeriya.

“Yan Najeriya su na bukatar shugaban kasar da bai da kabilanci ko nuna banbamcin addini ko jinsi, sannan ya zakulo zakuraran mutane masu tarin baiwa.”

“Wasu daga cikin halayen Jonathan na-gari su ne ikon raba kudi daidai wadaida a cikin al’umma, hakurinsa, kaunar zaman lafiya, sanin lafiya da kuma adalci.”

KU KARANTA: Doyin Okupe ya bada sanarwar zai nemi kujerar Shugaban kasa

Dawo-dawo: Magoya-baya sun fara yi wa Jonathan yakin neman zaben Shugaban kasa
Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan
Source: Twitter

A cewar Brown da Ebi, Dr. Jonathan ya san yadda ake mu’amala da mutanen gida da kasar waje.

Jawabin ya ce: “Mu na kira ga ‘yan siyasa daga Kudu da Arewa, su ba shi dama ya karasa wa’adinsa na shekaru hudu, wanda sauran bangarori su ka samu.”

A jiya mu ka samu labari cewa Mai girma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi zama da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya samu shawarar manya.

Wasu sun dage su na zugo Gwamna Yahaya Bello ya yi takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa. Ana ganin cewa gwamnan ya na cikin matasan da su ka samu mulki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel