Za mu binciki kamfanin Alpha-Beta da Ocean Trust nan ba da jimawa ba – Inji EFCC

Za mu binciki kamfanin Alpha-Beta da Ocean Trust nan ba da jimawa ba – Inji EFCC

Mun samu labari daga Jaridar nan ta Punch cewa kungiyoyi kusan 150 da ke yunkurin yaki da rashin gaskiya a Najeriya sun nemi a binciki wasu kamfanoni wanda su ka hada da Alpha Beta da Ocean Trust.

Za mu binciki kamfanin Alpha-Beta da Ocean Trust nan ba da jimawa ba – Inji EFCC
Mai magana da yawun bakin EFCC yace za a binciki kamfanin Alpha Beta
Asali: UGC

Kungiyoyin da ke yakar cin hanci da rashawa sun hurowa Hukumar EFCC wanda ita ce ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon-kasa wuta cewa ta gudanar da bincike game da badakalar da ake zargin wadannan kamfanonin da su.

Ana zargin cewa babban Jigon Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu shi yake da daya daga cikin wadannan manyan kamfanoni. Ana zargin cewa kamfanin ba ya biyan haraji sannan kuma ana amfani da shi wajen karkatar da kudi.

Wani tsohon Shugaban kamfanin Alpha Beta watau Dapo Apara ya zargi kamfanin da kin biyan haraji na kudin da su ka haura Naira Biliyan 100. Wannan ya sa Olanrewaju Suraju wanda shi ne Shugaban CSNAC ya nemi ayi bincike.

KU KARANTA: Buhari ya ba mutanen da su ka kashe kamfanin jirgin saman Najeriya mukamai a Gwamnati

Shugaban Kungiyar ta CSNAC mai yaki da masu satar dukiyar kasa yana neman Hukuma ta binciki zargin da ake yi wa kamfanonin na Alpha Beta da Ocean Trust wadanda su kadai ne aka ba lasisin karbar haraji a fadin Jihar Legas.

Ana zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu shi ne ya mallaki wannan kamfani wanda sun dade su na aiki da Gwamnatin Jihar ta Legas inda ake tunani su ke zaran kashi 10% na harajin da aka tara a Jihar mai arziki.

Gwamnatin Legas dai tayi gum game da zargin amma Jami’in da ke magana da yawun Hukumar EFCC ya nemi jama’a su kara hakuri inda ya tabbatar da cewa za a binciki wadannan kamfanoni a nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel