Apara ya na karar Tinubu a kotu bisa zargin da ke kan kamfanin Alpha-Beta

Apara ya na karar Tinubu a kotu bisa zargin da ke kan kamfanin Alpha-Beta

- Oladapo Apara ya shigar da kara kan kamfanin Alpha-beta consulting L.L.P

- Mista Apara ya taba aiki har ya kai Darekta a wannan kamfani da ke Legas

- Apara ya na zargin Alpha-beta da kauracewa biyan kudin haraji a Najeriya

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa an kai tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, kara gaban babban kotun da ke Legas.

An bukaci Bola Ahmed Tinubu ya hallara a gaban kotun na jihar Legas nan da kwanaki 42.

Wanda ya shigar da karar shi ne Oladapo Apara daga kamfanin Infiniti Systems Enterprises. Sauran wadanda ake tuhima su ne kamfanin Alpha-Beta.

Jaridar ta ce an gabatar da wannan kara ne tun a ranar Juma’ar da ta wuce, 2 ga watan Oktoba, 2020 a gaban Alkalin kotun da ke Igbosere, jihar Legas

KU KARANTA: Za mu binciki kamfanin Alpha-Beta - EFCC

Mai karar ya na so a tursasawa kamfanin Alpha-beta consulting LLP ya bayyana duka harkar kudin da ya shiga tsakaninsu daga shekarar 2010 zuwa yau.

Ana zargin arzikin kamfanin Alpha-beta consulting LLP ya bunkasa sosai tun bayan da aka ba su kwangilar karbar haraji a madadin gwamnatin jihar Legas.

Apara ya na zargin cewa Alpha-beta sun saba yarjejeniyar da su ka yi da kamfaninsa na Infiniti Systems Enterprises, su ka daina biyansa kason kudinsa.

A dalilin haka Mista Oladapo Apara ya tafi gaban hukumar EFCC, ya shaida mata cewa kamfanin Alpha-beta LLP ba su biyan haraji kamar yadda ya kamata.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun kama tsohon Gwamnan Imo da laifin sata da karya

Apara ya na karar Tinubu a kotu bisa zargin da ke kan kamfanin Alpha-Beta
Bola Tinubu Hoto: Wikipedia
Asali: UGC

Apara wanda ya rike Darekta a kamfanin Alpha-beta, ya shaidawa jaridar Punch cewa Bola Tinubu ya taba cika bakin cewa Ibrahim Magu zai kare shi.

Sai dai kuma yanzu an dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin EFCC, an kai karar kamfanin.

Tun 2018 wani Lauya ya bankado asirin kamfanin Alpha Beta. Ana tunani wannan kamfani ya na samun daurin gindi daga Gwamnati wajen gujewa biyan haraji.

An dade ana zargin kamfanin da keta dokokin safarar kudi da kuma kin biyan Gwamnati harajin fiye da Naira Biliyan 100, amma har yanzu ba a binciki lamarin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng