2023: Bukola Saraki ya fito ya fadi sirrin tattaunawarsu da Olusegun Obasanjo

2023: Bukola Saraki ya fito ya fadi sirrin tattaunawarsu da Olusegun Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya gana da tawagar Tsohon mataimakin shugaban majalisa

- Bukola Saraki da wasu jiga-jigan PDP sun kai wa tsohon shugaban kasar ziyara

- Saraki ya yi karin-haske, ya fayyace abin da ya kai kwamitinsa gaban Obasanjo

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya zauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a garin Abeokuta, jihar Ogun.

Dr. Bukola Saraki ya yi karin haske a game da abin da zaman su da tsohon shugaban kasar ya kunsa. Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoto a yau, Laraba.

Da aka yi hira da Bukola Saraki bayan shi da wasu manyan PDP sun sa-labule da Olusegun Obasanjo, ya ce su na kokarin yi wa jam’iyyar garambawul ne.

Jaridar ta ce an yi wannan zama ne a dakin karatun da Olusegun Obasanjo ya gina a Abeokuta.

KU KARANTA: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo

“Mun fada wa shi (Obasanjo) abin da mu ke kokarin yi, mu yi wa jam’iyya garambawul, mun fada masa amfanin wannan aiki a wajen gyara kasar nan.” Inji Saraki.

Saraki yake cewa: “Ya fada mana a shirye yake wajen ganin Najeriya ta cigaba, ya na cewa ba zai taba yin kasa a gwiwa a kan abin da zai sa kasar nan ta cigaba ba.”

“Shakka babu kamar yadda duk mu ka sani, shi (Obasanjo) bai nuna banbamcin siyasa a halin yanzu, abin da ke gabansa shi ne Najeriya, ba jam’iyya ba.” Inji sa.

Tsohon gwamnan wanda ya taba aiki a matsayin mai ba Obasanjo shawara a lokacin ya na shugaban kasa ya ce Obasanjo ya tuna masu bai da bangare a siyasa.

KU KARANTA: Akwai wasu katobara da Buhari ya ke yi – Obasanjo a wasikarsa

2023: Bukola Saraki ya fito ya fadi sirrin tattaunawarsu da Olusegun Obasanjo
Bukola Saraki Hoto: Majalisa
Source: Instagram

A jawabinsa, Saraki ya yi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi amfani da ‘yan adawa wajen yakin da ake yi domin kawo tsaro da zaman lafiya a kasar.

A baya kun ji Saraki wanda shi ne shugaban kwamitin sulhu da PDP ta kafa ya jagoranci Ibrahim Hasan Dankwambo, Olagunsoye Oyinlola, da Liyel Imoke zuwa Abeokuta.

Sauran ‘yan wannan kwamiti su ne: Ibrahim Shema da tsohuwar ‘yar majalisa, Mulikat Akande Adeola.

Idan ba ku manta ba, Obasanjo, wanda ya yi mulki a karkashin jam'iyyar PDP, ya keta katinsa na zama 'dan jam’iyya gabanin zaben 2015 da Goodluck Jonathan ya sha kashi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel