Obasanjo ya rubutawa Shugaba Buhari sabuwar doguwar budaddiyar wasika a kan matsalar tsaro

Obasanjo ya rubutawa Shugaba Buhari sabuwar doguwar budaddiyar wasika a kan matsalar tsaro

- Olusegun Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Tsohon shugaban kasar ya na ganin ‘buda wuta’ ba zai kawo karshen Boko Haram ba

- Obasanjo ya na tare fitaccen malamin addinin musulunci, Gumi, na zama ayi sulhu

A wani karon kuma, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aika wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari, Desert Herald ta rahoto wannan.

Olusegun Obasanjo ya gargadi gwamnatin Muhammadu Buhari cewa karfin bindiga kadai ba zai iya kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da shi ba.

Jaridar ta ce ra’ayin tsohon shugaban Najeriyar ya zo daidai da na Sheikh Ahmad Gumi wanda yake ganin sulhu ne zai kawo karshen wannan matsala.

Budaddiyar wasikar ta yi ba shugaba Muhammadu Buhari shawara cewa sulhu ce hanya mafi sauki da za a bi ayi maganin halin da al’umma su ke ciki.

KU KARANTA: Buhari: Kan ƴan Najeriya sun rabu, babu kan-ta - Obasanjo

Olusegun Obasanjo ya kuma bayyana cewa ana buga labaran bogi da sunansa saboda neman suna.

Tsohon mai gidan shugaban kasar ya ce amma hakan ba zai hana shi ya fito ya fada masa abin da ke cikin zuciyarsa ba, saboda girman lamarin rashin tsaro.

Obasanjo ya ce idan mutane su ka kai matakin da ba ba su yarda gwamnati za ta iya kare su ba, to za su tashi da kansu, su nemi mafita ta kowace irin hanya.

Haka zalika tsohon shugaban kasar ya zargi gwamnatin tarayya da yi wa al’ummar Najeriya karya a kan murkushe ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Obasanjo ya rubutawa Shugaba Buhari sabuwar budaddiyar wasika a kan matsalar tsaro
Shugaban kasa Buhari da Obasanjo Hoto: desertherald.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun fi sauraron Sheikh Gumi a kan gwamnati - Lai

Ya ce: “Boko Haram ba za ta kare da makami ba kurum, dole a zauna a tattauna. Ya za ka yi da matsalar rashin ilmi da rashin aikin yi a Arewa maso gabas.”

Obasanjo ya ambaci wasu kura-kurai da gwamnatin nan ta ke yi, daga ciki akwai sakaci da ta’adin Makiyaya da kuma kai wa Fulani hari da barkewar rikici.

A baya wasu kungiyoyi sun yi wa Malamin addini, Ahmad Abubakar Gumi raddi na kamanta ‘Yan bindigan da ke ta'adi a Arewa da kuma tsagerun Neja-Delta.

Kungiyar Pan Niger Delta Forum wanda aka fi sani da PANDEF, ta yi magana game da wasu kalamai da Sheikh Ahmad Gumi ya yi kwanaki, ta yi tir da shi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel