2019: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo

2019: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, a yau Laraba 30 ga watan Janairu, ya sake jaddada goyon bayan sa ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Mun samu cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce yana da yakinin cewa Najeriya za ta samu kyakkyawan ci gaba a karskashin jagorancin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Obasanjo ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku na da duk wata cancanta gami da nagarta ta fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira muddin ya yi nasara a yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe.

2019: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo

2019: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo
Source: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasar ya yi furucin hakan ne cikin wata sanarwa yayin gabatar da jawaban sa a wani taron harkokin kasuwanci na shekarar 2019 da aka gudanar a jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriiya ya ruwaito cewa, Atiku ya gabatar da na sa jawaban inda ya zayyana kudiri da kuma manufofi gami da tsare-tsaren sa na jagoranci yayin da kasar Najeriya ta kasance karkashin akala ta gudanarwar sa.

Cikin jawaban sa Obasanjo ya ce, ya na da aminci mai girman gaske dangane da cancantar, kwarewa da kuma kishin kasa da ya mamaye zuciyar Atiku wajen tabbatar da Najeriya da koma bisa turba da kuma tafarki na nagarta da aminci.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku, Saraki da Obasanjo yayin bayyana kudirin jam'iyyar PDP a jihar Legas

Yayin hikaito yadda takun saka da rashin fahimtar juna suka yi kamari tsakanin su a baya, Obasanjo ya ce Atiku a halin yanzu ya fahimci kura-kuran sa da tuni ya yayyafa ma sa ruwan afuwa kuma ya na kira ga al'ummar Najeriya su goya ma sa baya.

Ya kara da cewa, an yi walkiya kuma Atiku ya tabbatar da tsayuwar dakan sa gami da daurin damara ta amintattun jagorori ta hanyar neman afuwa tare da nadama a bisa kuskuren da ya aikata a baya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel